Cikas din da Tinubu zai fuskanta a zaben 2023 | Aminiya

Cikas din da Tinubu zai fuskanta a zaben 2023

Jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu
Jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu
    Ismail Mudashir da Muhammad Aminu Ahmad

Batun takarar Shugaban Kasa a badi ya dauki sabon salo a ranar Litinin din makon jiya, lokacin da jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar Shugaban Kasa.

Ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da ya yi da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, tsohon Gwamnan na Jihar Legas ya zama mutumin da aka fi magana a kansa a siyasar kasar nan.

Akwai batutuwan da suke kewaye da shi -masu kyau da marasa kyau da ake ta tattauna su a shafukan sada zumunta da kafafen watsa labarai.

Gwamnan Jihar Ebonyi, Mista Dabe Umahi ma ya bayyana aniyarsa ta son tsayawa takarar shugabancin kasar kwana daya, bayan Tinubu ya bayyana manufarsa kuma duk a wuri guda, wato a fadar Shugaban Kasa, sai dai masana na ganin hakan ba zai sanyaya gwiwar Tinubu da ake ganin gogarma ne.

Ana daukar Asiwaju a matsayin Sarkin Karaga mai nada Sarki a Jam’iyyar APC saboda rawar da ya taka wajen samun nasarar Shugaba Buhari a shekarar 2015 da kuma tasirin da ya yi a shiyyar Kudu maso Yamma, musamman Jihar Legas, inda ya rika samar mata da gwamnoni tun daga lokacin da wa’adinsa ya kare.

Yayin da akasarin wadanda suka yi Gwamna a tsakanin 1999 zuwa 2007 suka samu matsala ko rasa tagomashi a siyasa,Tinubu ya ci gaba da jan zarensa tare da fadada daulal siyasarsa zuwa sauran sassan kasar nan, abin da masu sharhi suke ganin wani yunkuri ne na cimma burinsa na zama Shugaban Kasa.

To sai dai kuma, don tabbatar da hakan, manazarta suna ganin dole ne ya tsallake wasu shingaye da za su iya kawo masa cikas da su hada da:

Samun goyon bayan Buhari don cimma burinsa

Masu lura da al’amuran siyasa, sun ce kafin Tinubu ya samu nasarar cim ma burinsa wajibi ne ya samu goyon bayan Shugaban Kasar.

Kuma rahotanni daga Fadar Shugaban Kasa suna nuna cewa kalaman da Shugaban ya yi ba su yi wa bangaren tsohon Gwamnan na Jihar Legas dadi ba.

“A gaskiya, abin da mutane suke tunani, shi ne an saka masa kan kokarin da ya yi a shekarar 2014/2015, ta hanyar bai wa nasa mukamin Mataimakin Shugaban Kasa da sauransu,” wata majiya ta kusa da Shugaban Kasar ta taba fadi a yayin tattaunawa kan burin Tinubu.

Wata majiyar Fadar Shugaban Kasar kuma ta ce akwai bukatar Tinubu ya jawo dan uwan Buhari Malam Mamman Daura, don cim ma burinsa.

“Kada ku damu da abin da (Mamman Daura) ya fada game da batun karba-karba a 2020, Asiwaju yana bukatar ganawa da shi. Don Shugaban Kasa ya fi saurarensa fiye da kowa,” inji majiyar.

Karya Gwamnoni 3 da Minista 1

A wata 19 da suka gabata juya akalar Jam’iyyar APC ta kasance a hannun wadansu gwamnoni uku ne da wani minista. Tun a watan Yunin 2020 da aka rushe Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar (NWC)a karkashin jagorancin Kwamared Adams Oshiomhole, jam’iyyar ta kasance a hannun Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, wanda ke shugabantar kwamitin riko da Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC da kuma Gwamna Badaru Abubakar na Jihar Jigawa.

Haka kuma an ce Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami na cikin kusoshin da suke juya akalar jam’iyyar.

A cewar manazarta, karyako samun hadin kan wadannan turaku uku da dirka daya ne shinge na biyu da Tinubu zai tsallake don kawar da abin da zai kawo cikas ga tafiyarsa.

Sanannan abu ne a jam’iyyar cewa wadansu jiga-jiganta sun yi nisa a yunkurinsu na ganin sun kawar da Tinubu daga takarar.

Majiyoyin jam’iyyar sun ce tsaikon da aka samu kan gudanar da Babban Taron Jam’iyyar ma na daga cikin makarkashiyar gwamnoni uku.

Kuma domin rage karfin tsarinsu masana harkar siyasa a jam’iyyar sun ce, “Ko dai Tinubu ya tabbatar an gudanar da Babban Taron Jam’iyyar, ko kuma a rushe kwamitin Buni cikin gaggawa.”

Shiyya-shiyya

Tun lokacin da kasar nan ta koma mulkin farar hula a 1999, aka fara karba-karbar mulkin a tsakanin Arewa da Kudu, duk da cewa ba tsarin mulkin ne ya tanadi hakan ba.

Sai dai masu lura da al’amura suna ganin jinkirin da ake samu wajen gudanar da Babban Taron jam’iyyar APC na daga cikin shirin baza takarar Shugaban Kasar nan a faifai ga kowa da kowa.

Duk da cewa a bara, Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Raji Fashola ya ce an yi yarjejeniyar mika mulki a tsakanin Arewa da Kudu wajen kafa jam’iyyar, amma an samu ce-ce-ku-ce kan lamarin a jam’iyyar.

A yanzu dai, majiyoyi sun ce akwai babban yunkuri na a bar tikitin takarar Shugaban Kasa a faifai ga kowa, ciki har da masu son tsayawa takara daga Arewa.

Wakilin matasa a Kwamitin Riko na Kasa na Jam’iyyar APC mai mambobi 13, Barista Isma’il Ahmed, a wata hira da aka yi da shi a kwanakin baya, ya ce hankalin jam’iyyar yana kan daidaitawa ne ba maganar karba-kaba ba.

“Kun san wannan batu na karba-karba bai taba zama wani abu irin wannan ba.

Kada ku manta cewa lamarin da ke gabanAPC lamarin ba maganar kaba-karba ba ce, gyara take nema na daidaitawa a tsakanin ’ya’yanta, ba lallai ba ne a hada da karba-karba ba.

“Saboda a zaben fid-dagwani na shekarar 2014, idan za a tuna, a watan Disamban 2014 da muka yi zaben fid-da-gwani da Shugaba Buhari ya samu nasara ai akwai mutum biyar da suka tsaya takarar Shugaban Kasa.

“Biyu ne kawai daga cikinsu suka fito daga shiyya daya, sauran kuma sun fito ne daga shiyyoyin siyasa daban-daban, misali Alhaji Atiku Abubakar (Arewa maso Gabas) sai marigayi Dokta Samu Nda Isaiah (Arewa ta Tsakiya); Rochas Okorocha (Kudu maso Gabas) da tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso na Jihar Kano da Shugaba Buhari (Arewa maso Yamma).

An fafata sosai a zaben,” in ji shi.

Masu fashin baki dai suna ganin Tinubu yana bukatar samun tikitin ne in aka mika wa Kudu kuma aka sake mika wa yankin Kudu maso Yamma kafin ya samu damar da yake bukata.

An kafa Jam’iyyar APC ce a shekarar 2013 bayan hadewar jam’iyyun CPC da ACN da ANPP da kuma wani bangare na Jam’iyyar APGA da kuma Sabuwar PDP (nPDP). Mataimaki da takarar Musulmi da Musulmi Wane ne zai zama mataimakin Tinubu idan ya samu tikitin APC?

Wannan ce babbar tambayar da take da wuyar amsawa ga masu tallata takararsa a Arewa da masu adawa da ita.

Kuma shi ma wani shinge ne mai wuyar tsallakewa ga Tinubu don kaiwa gaci.

Babban dalilin da ya hana Tinubu zama mataimakin dan takarar Shugaba Buhari a 2015 shi ne kasancewrsa Musulmi.

Duk wani kokari na ganin hakansa ya cim ma ruwa abin ya faskara, ganin cewar Buhari Musulmi ne kuma shi ma Tinubu Musulmi ne, hakan ta sa a karshe jiga-jigan jam’iyyar suka ba shi damar ya kawo wani Kirista da za su yi tafiyar tare da Buhari.

Hakan ne ya kai ga fitowar Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin Mataimakin Buhari. Yanzu ma irn wannan yanayi ya sake tasowa.

Jigajigan jam’iyyar musamman gwamnoni da suke son zama mataimakinsa Musulmi ne.

“Wannan yana daya daga cikin dalilan da wadansu jigajigan jam’iyyar biyu suke adawa da takararsa. To, wa zai dauka? Idan ya zabo Musulmi, zai jawo nakasu ga makomar jam’iyyar a yayin zaben. Haka idan ya dauki Kirista ba zai je ko’ina ba,” inji wani dan jam’iyyar.

Kalubalen rashin lafiya

Haka masu adawa da takarar jagoran Jam’iyyar APC na Kasa suna amfani da batun rashin lafiyarsa wajen bata shi. Suna gargadin kada a maimaita irin abin da ya faru da Buhari.

A zangonsa na farko, Shugaba Buhari ya rika zuwa Landan domin neman magani, inda ya shafe watanni a daya daga cikin irin wadannan tafiye-tafiye na jinya. Tsakanin watan Agusta da Oktoban bara, Tinubu ya tafi Landan, domin kula da lafiyarsa. Buhari da Tinubu sun je Landan domin jinya a bara.

Yayin da Buhari yake can na wasu kwanaki, Tinubu ya shafe watanni da dama. Har ma Buhari ya ziyarce shi. Bayan ziyarar Shugaban Kasar ne a gidan Tinubu da ke Duchess Mews, Portland Place, a tsakiyar Landan, sai kuma gidan ya zama wurin da kowa ke kai ziyara, inda yaransa na siyasa da masoyansa da magoya bayansa suka yi ta tururuwar kai masa ziyara.

Duk da cewa abokan Tinubu sun ce ya je an yi masa tiyata ce a gwiwa, wadanda suke adawa da takararsa sun rika bayar da wasu dalilan na daban.

Masu sa ido a kan harkokin siyasa suna nanata bukatar da ke akwai ta tsohon Gwamnan ya fito ya bayyana hakikanin yanayin lafiyarsa.

Sai dai wani mamba a Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC), Sanata Magnus Abe, ya yi watsi da rade-radin da wadansu ke yi cewa Tinubu ya tsufa kuma ba shi da cikakkiyar lafiyar da zai iya zama Shugaban Kasa, inda ya ce ba dole ba ne shekaru su zama ma’auni wajen shugabanci.