✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cin gwaza kariya ce daga cutar suga da COVID-19 —RMRDC

Binciken hukumar RMRDC ya ce cin makani na samar da sunadaran kariya ga jikin dan Adam.

Hukumar Bincike da Inganta Kayan da ake Sarrafawa (RMRDC) ta ce cin makani na samar da sinadaren da ke ba jikin dan Adam kariya daga kamuwa da cutar suga da kuma COVID-19.

Darakta-Janar din RMRDC, Ibrahim Hussaini Doko ne ya sanar da hakan a wurin taron kaddamar da wani littafi mai suna, ‘Gwaza: Abinci mai samar da sunadarai da kuma kariya daga cutar suga,’ a Abuja ranar Alhamis.

Doko wanda ya samu wakilcin Darantar Bunkasa Masana’antu na Hukumar, Dokta Bola Olugbemi, ya ce gwaza na dauke da sunadarin glycerin, kuma cin sa musamman da manja ko gyara na rage yawan suga a jiki.

“Cin gwaza na da amfani mai yawa ga lafiya, daga ciki, yana ba da kariya daga cutar suga. Yana kuma rage hadarin daukar cutar COVID-19.

“Gwaza na dauke da sunadarin glycerin wanda ba ya illa ga jiki kamar sukari kuma ba ya sa yawan sugan jiki ya karu,” kamar yadda ya bayyana.

Ya kara da cewa RMRDC za ta zurfafa bincike domin gano wasu amfanin cin gwaza da kuma hanyoyin da za a inganta noman sa.