‘Cin zarafin mata ya karu sosai a Kano cikin watan Mayu’ | Aminiya

‘Cin zarafin mata ya karu sosai a Kano cikin watan Mayu’

Miji da matarsa
Miji da matarsa
    Rahima Shehu Dokaji

Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa da Ci Gaba (CITAD) ta ce a Jihar Kano, an samu karuwar cin zarafin mata a watan Mayun 2022, fiye da watannin baya.

Ta bayyana hakan ne yayin gabatar da rahoton da take fitarwa bayan tattara alkaluma a kowanne wata.

A watan na Mayu dai, CITAD ta ce korafin da ya fi daukar hankalinta shi ne na wata daliba da ta shigar da korafin fadar da daliban da suka samu nasara a jarabawa da wani malaminsu yayi a kwalejin Ilimin Shari’a da Addinin Musulinci da ke Kano ta yi, in da ta nemi cibiyar ta sa hannu a lamarin.

Babban Daraktan cibiyar, Dokta Yunusa Zakari Ya’u ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da cibiyar ta shirya a Kano.

Ya ce wannan guda ne daga cikin korafe-korafe 35 da aka turawa cibiyar ta manhajar da ta ware g al’umma domin yin hakan.

korafe-korafen da cibiyar ta ce ta tattaro ta manhajar a watan na Mayu sun hada da cin zarfi ta intanet da batancin suna da dukan mata daga mazajensu da kuma cin zarafin dalibai.

Babban Daraktan ya ce akwai bukatar gwamnati ta kara kaimi domin kawo karshen wadannan matsalolin da ke dakushe mata a cikin al’umma ta hanyar samar da tawagar da za ta dinga bibiyar laifukan musamman a shafukan intanet domin kamo masu aikata su.