✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

City ta karbe ragamar teburin Firimiyar Ingila daga hannun Arsenal

Yanzu City tana da maki 76 kuma tana da kwantaan wasa daya.

Manchester City ta karbe ragamar teburin Gasar Firimiyar Ingila daga hannun Arsenal bayan ta doke Fulham da ci 2-1 a wasan da suka yi ranar Lahadi.

City dai ta zama ta daya a saman teburin a karon farko cikin watanni biyu.

Julian Alvarez da Erling Haaland ne suka zura kwallayen biyu kuma kwallon da Haaland ya zura ita ce ta 50 da ya ci a kakar wasa ta bana a dukkan gasa da ya fafata.

Kazalika dan wasan na kasar Norway ya yi kankankan da wasu magabatansa wurin zura kwallo a gasar Firimiya a kaka daya – inda ya ci kwallo 34, daidai da adadin da Andy Cole ya ci wa Newcastle a 1993-94 da kwallayen da Alan Shearer ya ci wa Blackburn shekara daya bayan haka.

Alvarez ya yi wa City wasa ne bayan an hana Kevin De Bruyne murza leda sakamakon raunin da ya ji, kuma bai bata lokaci ba wajen taka rawa a filin wasa.

Fulham ta zura kwallo ta hannun Alves Morais a minti 15 da soma wasan.

Yanzu City tana da maki 76 kuma tana da kwantaan wasa daya, yayin da Arsenal ke biye mata da maki 75.

Wannan ne karon farko da City ta sha gaban Arsenal tun tsakiyar Fabrairu a yayin da take fafutukar lashe Kofin Gasar Firimiya da na Zakarun Turai da kuma na FA.