✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Gwamnan Legas ya yi addu’ar Easter a gida

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya ba da sanarwar cewa ya yi addu’ar ranar Easter ta internet a gida tare da maidakinsa. “Na yi addu’ar…

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya ba da sanarwar cewa ya yi addu’ar ranar Easter ta internet a gida tare da maidakinsa.

“Na yi addu’ar Easter tare da uwargidana a gida, mun yi wa iyalinmu addu’a da jihar mu ta Legas da ma kasa baki daya”, inji shi.

Gwamnan ya bayyana haka ne ta kafofin sada zumuntarsa inda ya yi kira da a ci gaba da kiyaye ka’aidojin hana yaduwar annobar coronavirus.

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu tare da maidakinsa sun yi addu’ar Easter a gida

A daidai lokacin da Kiristoci a fadin duniya ke bukin Easter, a bana annobar coronavirus ta hana gudanar da addu’o’in yadda aka saba.