✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: An sake samun sabon samfurin Omicron mai wahalar ganewa

Binciken na zuwa ne lokacin da yawan wadanda suka kamu suka kai 6 a Najeriya.

Masana ilimin kimiyya a Birtaniya sun ce sun sake gano sabon samfurin cutar COVID-19 na Omicron mai wahalar banbancewa daga sauran samfuran cutar da ke ci gaba da yaduwa a sassan duniya daban-daban.

Binciken na zuwa ne a daidai lokacin da yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya ya kai mutum shida.

Sabon samfurin dai na da kamanceceniya da na Omicron, amma kayayyakin gwaje-gwajen ragowar samfuran ba su cika gano ta cikin sauki ko da an yi gwajinta.

Ko da yake, gwajin ya kan nuna ta a matsayin COVID-19, amma ainihin gwajinta na nuni da cewa ta banbanta da ita.

Sai dai masu bincike sun ce ya yi wuri a gane ko sabon samfurin na Omicron zai ci gaba da yaduwa da gaggawa kamar sauran, amma dai sun tabbatar da cewa ya banbanta da ragowar.

An dai fara gano sabon samfurin ne a wasu gwaje-gwaje da aka yi kwanan na Afrika ta Kudu, Australiya da kuma Kanada, amma akwai yiwuwar ta yadu zuwa wasu kasashen da dama.

Binciken masanan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Firministan Birtaniya, Boris Johnson ya shaida wa Majalisar kasar cewa samfurin Omicron na da alamar saurin yaduwa fiye da sauran, kuma akwai yiwuwar a sake daukar tsauraran matakai wajen dakile ci gaba da bazuwarta.