✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Covid-19: Mutum 138 ne suka warke a Legas

Gwamnatin jihar Legas ta sallami karin mutum 15 da suka warke daga annobar coronavirus. Daya daga cikin su dan kasar Indiya ne, yayin da ragowar…

Gwamnatin jihar Legas ta sallami karin mutum 15 da suka warke daga annobar coronavirus.
Daya daga cikin su dan kasar Indiya ne, yayin da ragowar 14 ‘yan Najeriya ne wadanda aka sallama a yau ranar  Litinin 27 ga watan Afrilu.

An sallame su ne daga inda da aka killace su a cibiyar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta IDH da ke Yaba da kuma wasun su daga cibiyar killace masu cutar da ke sitadiyom ta Mobolaji Johnson.

Sanarwar wacce Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu da ma’aikatar lafiya ta jihar suka fitar a shafinsu na tweeter ta bayyana cewa 11 daga cikin mutanen da suka warke a wannan karon mata ne, 4 kuma maza.

Kawo yanzu dai mutum 138 ne suka warke daga coronavirus a jihar Legas.