✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19: NAFDAC ta amince da rigakafin Pfizer

NAFDAC ta amince da yin rigakafin COVID-19 na kamfanin Pfizer a Najeriya

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta amince da rigakafin cutar COVID-19 na kamfanin Pfizer.

Darakta-Janar ta NAFDAC, ta bayyana a Legas, ranar Juma’a cewa Hukumar ta amince da yin amfani da rigakafin kamfanin a Najeriya a matakin gaggawa.

Sahalewar rigakafin Pfizer na zuwa ne watanni kadan bayan NAFDAC ta ba da izinin yin rigakaficin cutar COVID-19 na Oxford-Astrazeneca a Najeriya.

Kawo yanzu, mutum miliyan 1.19 ne aka yi wa rigakafin cutar ta COVID-19 a Najeriya.

Hukumar Kula da lafiya a matakin farko ce ke sanya ido kan gudanar da allurar rigakafin cutar cikin aminci a madadin Gwamnatin Tarayya.