✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘COVID-19 ta kashe ’yan jarida sama da 600 a duniya’

Wani bincike ya nuna cewa sama da ’yan jarida 600 ne suka mutu sanadiyyar cutar COVID-19 a fadin duniya.

Wani bincike ya nuna cewa sama da ’yan jarida 600 ne suka mutu sanadiyyar cutar COVID-19 a fadin duniya.

Wata kungiya mai rajin kare hakkin ’yan jarida (PEC) wacce ta tattaro alkaluman ’yan jaridar da lamarin ya shafa ta ce akalla mutum 602 ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin da kimanin 303 daga cikin adadin suka fito daga kasashen yankin Latin Amurka.

Kazalika, kungiyar ta ce 145 sun mutu a nahiyar Asiya, 49 a Turai, 32 a Arewacin Amurka sai kuma 28 a Afirka.

Kungiyar, wacce ke da zama a Geneva ta ce kamata ya yi a ba ma’akatan kafafen watsa labarai fifiko wajen bayar da rigakafin cutar a kasashen duniya.

“Saboda yanayin aikinsu, ’yan jarida dake shiga lungu da sako wajen zakulo labarai na jefa rayuwarsu cikin hatsarin kamuwa da cutar. Wasu daga cikinsu, musamman masu zaman kansu da masu daukar hoto ba zai yuwu su yi aiki daga gida ba,” inji Babban Sakaaren kungiyar, Blaise Lempen a wata sanarwa.

PEC ta ce ta tattara alkalumanta ne daga kafafen watsa labarai na kasashe daban-daban, kungiyoyin ’yan jaridu na kasashe da kuma wakilan kungiyar na yankuna.

A bangaren daidaikun kasashe kuwa, binciken ya ce kasar Peru ce a kan gaba da mutum 93, sai Brazil dake biye mata baya da 55, Indiya 53, Mexico 45, Ecuador 42, Bangladesh 41, Italiya 37 sai kasar Amurka mai 31.