✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19 ta sake bulla a Kano, ta kashe mutum biyu

Mutum 2 sun mutu, 21 sun kamu a rana guda, bayan sake bullar cutar a Jihar Kano.

Mutum biyu sun mutu wasu 21 kuma sun kamu da cutar COVID-19 a Jihar Kano a rana guda.

Bayan tsawon lokaci babu cutar a Jihar Kano, Shugaban Kwamitin Yaki da COVID-19 na jihar, Tijjani Hussaini, ya ce a kwanaki 10 da suka gabata kadai an gano mutum 85 da suka kamu da ita a jihar.

“Yaduwar COVID-19 na yawaita musamman a watan Disamba inda mutum 85 suka kamu a kwana 10. A rana guda kacal ta kashe mutum biyu ta kuma kama wasu 22, wato ranar Alhamis”, inji shi.

Ya ci gaba da cewa: “An gano yawancin wadanda suka kamun ne a Karamar Hukumar Karaye saboda sansanin horas da masu yi wa kasa hidima (NYSC); don haka dole a yi wa kowane mai yi wa kasa hidima gwaji”.

Ya ce a kananan hukumomin Nasarawa da Birni da ma wasu kauyuka an samu sabbin masu cutar ta coronavirus, don haka ya yi kira ga jama’ar jihar da su kiyaye matakan kariyarta.

COVID-19: Kano ta yi wa ma’aikatan COVID-19 kiranye

Tuni Gwamna Abdullahi Ganduje ya ba da umarnin yi wa jami’an lafiya da suka yi aikin sa-kan yaki da COVID-19 kiranye domin sake yakar ta.

Ya ce gwamnatin jihar za ta sake zage damtse ta hanyar amfanin da dukkannin abubuwan da suka dace don murkushe cutar a jihar.

Ganduje ya kuma bayyana damuwarsa game da yadda jama’a suka yi watsi da sanya takunkumi, ba da tazara, wanke hannu da sauran matakan kariyar cutar.

“Mun sake faro shiri saboda COVID-19 ta dawo, don haka tilas ne mu mike mu yake ta a cikin al’ummomi musamman ta hanyar sanya takunkumi da kuma aiwatar da matakan kariya.

“Za mu yi wa ma’aikatan lafiya na wucin gadi kiranye domin yakar cutar yadda muka yi a baya,

“Sannan za mu hada kai da masu ruwa da tsaki kamar malaman addini don ci gaba da wayar da kan al’umma kan bayar da tazara, sanya takunkumi da kuma wanke hannu”, inji Ganduje.