✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da ya kashe mahaifiyarsa a Neja ta hanyar banka mata wuta

Rahotanni sun ce dama a baya ya jima yana yunkurin hallaka ta.

Da ga tsohuwar Shugabar makarantar Sakandiren Gwamnati ta ’Yan Mata da ke Sabon Wuse a Jihar Neja, Misis Confort Jiya, ya banka mata wuta har sai da ta mutu.

Matar kuma ta taba zama Shugabar Kwalejin Kimiyya ta Maryam Babangida da ke Minna, babban birnin Jihar.

Rahotanni sun ce matashin, mai suna Steven, wanda ke ta’ammali da miyagun kwayoyi, ya banka mata wutar ne jim kadan da dawowarsa daga Suleja ranar Litinin.

Lamarin ya faru ne a gidan matar da ke unguwar Darussalam a birnin Minna.

Wata majiya daga dangin matar ta shaida wa Aminiya cewa Steven ya iske mahaifiyar tasa ne a dakin girki, inda bai yi wata-wata ba ya antaya mata fetur inda nan take ta kama da wuta.

A cewar majiyar, marigayiya Comfort ta rasu ne ranar Juma’a da misalin karfe 3:00 na yamma a asibitin da take jinya.

Kazalika, wata majiyar ta shaida wa wakilin namu cewa matashin ya jima yana yunkurin hallaka ta, amma bai sami nasara ba sai a ranar ta Litinin da ya kona ta.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’Yan Sandan Jihar, DSP Wasiu Abiodun, don yin tsokaci a kan lamarin, hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

Amma Aminiya ta gano cewa tuni Babbar Kotu da ke Minna ta aike da Steven gidan gyaran hali bayan da ’yan sanda suka gurfanar da shi a gabanta.