✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DAGA LARABA: Amfani Da Illar Shafukan Zamantakewar Aure Na Intanet

Shin kwalliya na biyan kudin sabulu a shafukan kyautata zamantakewar aure na kafofin sada zumunta?

More Podcasts

Ku latsa nan domin sauraron shirin a lokacin da kuke so.

Cigaban zamani ya sa an koma amfani da kafofin sada zumunta wajen yin wasu abubuwa da a baya ake yin su a zahiri, ciki har da neman shawarwarin kyautata zamantakewar aure.

Shin shafukan kyautata zamantakewar aure gyara suke yi ko barna? Mece ce kwarewar masu gudanar da su kuma shin kwalliya na biyan kudin sabulu ga masu bin su?

Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi nazarin irin wadannan shafuka da irin tasirinsu wurin ingantawa ko lalata zamantakewa.