✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Daga yanzu kauyuka za mu rika tura masu yi wa kasa hidima a Jigawa’

NYSC ta ce ta yanke shawarar ne a irin yunkurin da take yi na bunkasa harkar ilimi a yankunan karkarar jihar.

Hukumar Kula da Matasa Masu yi wa Kasa Hidima (NYSC) reshen jihar Jigawa ta ce daga yanzu kaso 90 cikin 100 na matasan da aka tura jihar makarantun yankunan karkara za ta aikewa da su.

Sabuwar shugabar hukumar a jihar, Hajiya Aishatu Adamu ce ta bayyana hakan lokacin da ta ziyarci ofishin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) dake Dutse ranar Litinin.

Hajiya Aisha wacce ta karbi ragamar jagorancin hukumar a jihar ranar takwas ga watan Afrilun 2021, ta ziyarci ofishin ne a wani bangare na irin ziyarce-ziyarcen kulla zumuncin da take kaiwa muhimman wurare dake da alaka da hukumar a jihar.

Ta ce, “Ina mai kara jaddadawa cewa matukar ina nan, zan tabbatar da cewa kaso 90 cikin 100 na matasa masu yi wa kasa hidima an tura su makarantun da ke da bukatarsu domin mu inganta harkar ilimi a jihar nan.”

Ta ce ta yanke shawarar ne a irin yunkurin da take yi na bunkasa harkar ilimi a yankunan karkarar jihar.

Kazalika, ta kuma jinjinawa NAN kan irin gudunmawar da yake ba NYSC a jihar ta hanyar ba da labaran ayyukanta a jihar.

Hajiya Aisha ta ce NYSC za ta sami wadanda suke da ilimin kimiyya daga cikin matasan da nufin basu horo sannan su rika aiki da ma’aikatan lafiya wajen yaki da COVID-19 a yankunan na karkara.

Da yake mayar da martani, wakilin NAN a jihar, Abdullahi Mohammed ya godewa shugabar dangane da ziyarar inda ya yi alkawarin ci gaba da samun cikakken hadin kai daga kamfanin.