✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daliba ta kashe kanta saboda lakcara ya daina son ta a Adamawa

Dalibar ta sha guba ne sakamakon rabuwa da malamin Kwalejin.

Wata dalibar Kwalejin Kimiyya  da Kere-Kere ta Tarayya da ke Mubi, Jihar Adamawa ta kashe kanta sakamakon rabuwa da saurayinta.

Dalibar mai shekara 24 tana karatun aikin jarida ne a Kwalejin kuma tana aikin daukar horo ne a gidan talabijin na Adamawa (ATV) da ke Yola.

Dalibar wacce ’yar asalin Garkida Gombi ce, an tsinci gawarta ne a dakinta da ke unguwar Hayin Gada, a Karamar Hukumar Girei a jihar.

Ana zargin ta sha guba ne sakamakon bakin cikin rabuwa da saurayinta.

Rahotanni sun bayyana cewa, saurayin Balami wanda malami ne a Jami’ar Modibbo Adama (MAU) ya bukaci su rabu, lamarin da ake ya sanya ta kashe kanta.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ya ce mahaifin dalibar ya kawo musu kara kan lamarin.

Kakakin ya ce rundunar za ta yi bincike domin gano musabbabin mutuwar dalibar.