✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalibai sun daina zuwa makaranta sun koma Harkar Yahoo

Firinsifal ta ce kashi 65 na daliban sakandaren gwamnati da ke yankin sun daina zuwa makaranta

Wata shugabar makaranar sakandare ta koka bisa yadda daliban makarantun gwamnati ke daina zuwa makaranta suna komawa harkar damfara a intaane, wanda aka fi sani da Yahoo-yahoo.

Misis Rita Kogeuonye, firinsifal din Makarantar Sakandare ta Owa-Alizomor a Karamar Hukumar Ika ta Gabas ta Jihar Delta, ta nuna damuwarta cewa yanzu kashi 65 na daliban sakandaren gwamnati da ke yankin sun daina zuwa makaranta.

Firinsifal Rita Kogeuonye ta shaida wa taron zauren al’ummar Owa-Alizomor karo na 17 cewa “Idan aka yi wa daliban magana su rika zuwa makaranta sai su ce ai zuwa makaranta bata lokaci ne kawai,  harkar yahoo ta fi riba a wannan zamani.

“Shi ne dalilin nake roko ku taya mu yi wa iyayensu magana, domin ’ya’yan nasu su ci gaba da zuwa makaranta, saboda ilimi na da matukar muhimmanci ga rayuwarsu.

Misis Rita ta kara da cewa bacin haka, wasu daga cikin daliban, sun sani cewa iyayensu ba su da karfin biya musu kudin makranta.

Don haka ta roki mahalrta taron da su taimakwa wajen farfado da dakunan gwaje-gwaje da dakin karati da dakin jarabawa da dakin gudanarwa da ke makarantar, wanda hakan zai taimaka wajen rage matsalolin da ke ci wa al’ummar tuwo a kwarya.

Da yake nasa jawabin, sakataren kungiyar cigaban al’ummar Owa-Alizomor, Fidelis Kisimkwu, ya yi alkwarin kungiyar za ta biya wa dalibai masu karamin karfi kudin makaranta da kuma magance matsalar da firinsifal din ta koka a kansu.

A cewarsa, za a kafa wani kwamiti da zai lalubo hanyoyin da za a rika ba wa yaran yankin kwarin gwiwar rungumar harkar neman ilimi.