✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalibai sun lakada wa malami duka saboda hana su satar jarrabawa

Irin haka dai ta faru kusan sau hudu a watan Oktoban 2021 a Jihar Ogun.

Akalla wasu dalibai 10 ne aka samu rahoton sun lakada wa malaminsu dukan tsiya saboda hana su satar jarrabawa a Jihar Ogun.

Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne ranar Talata a wata makarantar sakandire ta Isanbi Comprehensive High School da ke Karamar Hukumar Ikenne ta jihar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, malamin mai suna Kolawole Shonuga ya kwace takardun daya daga cikin daliban bayan ya kama shi yana satar amsa a lokacin da yake tsaron ’yan aji hudu (SS1) da ke zana jarrabawar zangon karshe na bana.

Sai dai bayan an tashi daga makarantar ne dalibin mai suna Ashimi Adebanjo ya hado kan abokansa inda suka yi kungiya suka dirar wa malamin a kofar makaranta kuma suka lakada masa duka.

Bayanai sun ce tuni lamarin ya shiga hannun hukuma, inda jami’an ’yan sanda suka cafke akalla dalibai 10 da ake zargi kamar yadda kakakin ’yan sandan Jihar Ogun, Omotola Odutola ya sanar.

Shugaban Kungiyar Jami’an Makarantun Sakandire na jihar, Felix Agbesanwa, ya bayyana fushinsa kan lamarin da cewa dole ne daliban su girbi abin da suka shuka.

Irin haka dai ta faru kusan sau hudu a watan Oktoban 2021, inda aka samu dalibai sun ci zarafin malamansu a makarantun Gwamnatin Jihar Ogun.