✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Daliban Yauri: Iyaye sun fara sayar da kadarorinsa don biyan fansar N100m

Naira miliyan 100 suke neman tarawa don kubutar da yaransu.

Iyayen daliban Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri a Jihar Kebbi sun fara sayar da gidajensu da suke ciki da gonaki da sauran kadarorinsu domin tattara kudin da za su kubutar da ’ya’yansu daga hannun ‘yan bindiga.

Iyayen yaran na neman tara Naira miliyan 100 don kubutar da ’ya’yansu mata da ke hannun ’yan fashin daji fiye da wata 20.

A ranar 17 ga Yuni, 2021 ’yan bindigar suka kai  hari makarantar suka sace daliban; Kodayake an kubutar da kaso mai yawa, amma har yanzu mutum 11 na hannunsu.

’Yan bindigar sun bukaci a biya su fansar miliyan N100 kafin su saki ’yan matan su 11.

Iyayen yaran sun yanke shawarar daukar matakin sayar da kadarorinsu don kubutar da ’ya’yan nasu ne bayan abin da suka kira rashin katabus na mahukunta a matakin kasa da jihar suka yi shuru kan batun.

Bayanai masu tushe sun nuna ’yan bindigar sun aure kusan baki daya yaran su 11, har wasunsu ma sun haihu.

A wani taron manema labarai da ya kira, shugaban iyayen yaran makarantar, Salim Kaoje, ya bukaci dauki daga daidaikun jama’a don ganin an ceto yaran.

Ya ce ba su da zabin da ya wuce neman agaji daga jama’a da kuma sayar da kadarorin da suka mallaka don ceto rayuwar yaran.