✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ƙungiyoyi ke rububin Xabi Alonso

Bayern da Liverpool na neman wanda za su bai wa kocin kungiyoyinsu a bazarar bana.

A makon jiya ne Shugaban Ƙungiyar Kwallon Kafa ta Bayern Munich, Mista Uli Hoeness ya bayyana cewa ƙungiyar ta kasar Jamus da Ƙungiyar Liverpool ta Ingila na fafautikar ɗaukar Xabi Alonso a matsayin mai horar da ’yan wasansu.

Idan ba a manta ba, Alonso ya buga kwallo a ƙungiyoyin biyu, kuma yanzu haka yana ta nuna bajinta a Ƙungiyar Bayer Leverkusen ta Jamus, inda yanzu haka ƙungiyar ta kama hanyar lashe kofin Gasar Bundesliga a karon farko a tarihinta.

Bayern da Liverpool na neman wanda za su bai wa kocin kungiyoyinsu a bazarar bana.

Aminiya ta gano cewa manyan ƙungiyoyin tamaula kamar Liverpool da Real Madrid, Bayern Munich da sauransu suna ruburin ɗaukar tsohon dan wasan.

Thomas Tuchel zai bar horar da Bayern Munich a karshen kakar wasa ta bana a yayin da shi ma Jurgen Klopp ya sanar da cewa zai bar horar da Liverpool a karshen kakar ta bana.

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya sabunta yarjejeniyarsa har zuwa shekara ta 2026, amma kuma an taba ruwaito cewa ƙungiyar ta riga ta zabi tsohon ɗan wasan nata a matsayin wanda zai maye gurbin Ancelotti.

Aminiya ta ruwaito Ancelloti yana yabon Alonso, inda yake kwatanta shi da matashin mai horarwa, wanda a cewarsa yake da yakinin zai iya jagorantar Ƙungiyar Real Madrid.

Alonso ya shafe shekara biyar a matsayin ɗan wasan Real bayan ya bar Liverpool sannan daga Real Madrid ya tafi Bayern Munich.

Haka kuma tsohon dan wasan ya taka leda a karkashin fitattun masu horar da ’yan wasan irin su Jose Mourinho a Ƙungiyar Real Madrid, da Guardiola a Bayern Munich da Rafael Benitez a Liverpool da Carlo Ancelotti a Real Madrid, da sauransu.

Sannan mahaifinsa tsohon dan wasa ne kuma koci a Sfaniya, wanda hakan ya sa yake da fahimtar harkar sosai.

Aminiya ta ci karo da wani faifan bidiyo, inda a ciki fitaccen koci Jose Mourinho yake bayanin cewa yana hango cewa Xabi Alonso zai zama ƙwararren mai horar da ’yan wasa saboda yadda ya fahimci harkar a filin wasa, da kuma yadda ya samu horo a wajen fitattun masu horar da ’yan wasa.

Kwantaragin Alonso a Leverkusen zai kare ne a shekarar 2026, sai dai tuni ya sanar da ƙungiyoyin da ke zawarcinsa cewa shi fa zama daram a Leverkusen.

Yanzu haka Bayern Leverkusen ta buga wasa 38 a duk gasanni ba tare da ta yi rashin nasara ba, inda ta yi dare-dare a saman teburin Gasar Jamus  da tazarar maki 11.

Wannan ya sa ake ganin zai yi wahalar gaske ƙungiyar ta gaza lashe gasar a bana.

A kakar bara, ƙungiyar ta kare ne a matakin na shida, sannan ta kai matakin wasan kusa da na qarshe a Gasar Kofin Europa.

Wannan ne karo na huɗu a Gasar Bundesliga da ake iya zuwa wasa 23 ba tare da rashin nasara ba.

Koci Die Werksell ya tava samun irin wannan nasara a ƙungiyar a kakar 2009/2010, sannan Bayern Munich ta samu irin hakan sau biyu.

Amma kaiwa matakin wasa 33 ba tare da rashin nasara ba, wannan ne karon farko da wata ƙungiya a Gasar Bundesliga za ta samu wannan nasara.

Ƙungiyar ta samu nasara a wasa 29, sannan ta yi kunnen doki a wasa huɗu a kakar bana.

Lokacin da Xabi Alonso ya karɓi horar da Ƙungiyar Bayern Leverkusen a Oktoban 2022, tana matakin na 17 ne a teburi.

Tun karɓar ragamar, yake ta samun nasara har zuwa yanzu da ya kama hanyar kafa tarihin lashe wa kungiyar kofin Gasar Bundesliga na farko.