✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da farashin shinkafa ya faɗi a Kano

Kayan gida ba sa sauka sosai. An fi samun sauƙin a na wajen.

Rahotanni na nuna cewa farashin shinkafa ’yar waje da ma wasu kayayyakin da ake shigo da su daga ƙetare ya faɗi a kasuwannin Kano.

A tattaunawarmu da wasu ’yan kasuwar da ke Singa, sun bayyana mana cewa farashin shinkafar waje, da dama daga kayan da ake shigowa da su daga ƙetare sun sauko.

Binciken Aminiya dai ya gano cewa shinkafar waje a Kasuwar Singa ana sayar da ita ne kan N66,500 daga farashinta na baya na N87,000.

Sai dai shinkafar gida ta Gerawa na nan akan farashinta na baya wato N63,000 zuwa sama.

A cewar Basiru Dauda Kunya, dan kasuwa a Kasuwar ta Singa, faɗuwar farashin kayayyakin na da alaƙa ne da farfaɗowar darajar Naira a kasuwar canjin kuɗi.

“Kayan gida ba sa sauka sosai. An fi samun sauƙin a na wajen,” in ji shi

Kan dalilin da ya sanya farashin kayan ba ya saurin faɗuwa kamar yadda yake saurin hawa da zarar dala ta tashi kuwa, Kunya ya ce matsalar daga wasu daga cikin ‘yan kasuwar ne.

“‘Yan kasuwar ne kala-kala muna tare da su ga su nan. Idan an samu sauƙin kayan ma sai su ce kayan da suka saya masu tsada ne, dole sai sun sun kare tukunnan sannan su sayo masu saukin.”