✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da masana’antun Kano ke kwan-gaba-kwan-baya

Adaidai lokacin da Najeriya ta yi bikin cika shekara 60 da samun ’yancin kai, ga dukkan alamu tana dada koma baya ne a fannin masana’antu…

Adaidai lokacin da Najeriya ta yi bikin cika shekara 60 da samun ’yancin kai, ga dukkan alamu tana dada koma baya ne a fannin masana’antu inda a ’yan shekarun da suka shude, akasarin masana’antun da kasar ke da su suka ruguje.

Masaku sama da 120 da kamfanonin harhada motoci shida da ake da su a sassan kasar nan da suka hada da Fiat a Kano da fijo (PAN) a Kaduna da Baswaja a Legas da Lyland a Ibadan da Anamco a Anambra da Kamfanin Takardu a Akwa Ibom da na taki a Fatakwal da matatun man fetur da sauran kanana da manyan masana’antu ko dai sun mutu murus ko kuma sun maqyarqyatar macewa.

Misali Jihar Kano kadai wadda ta shahara a harkar masana’antu a qasa baki daya ta rasa dubban masana’antunta. Binciken Aminiya ya gano cewa a shekara 20 baya, akwai kamfanoni masu aiki akalla 1,000 zuwa 1,500 a Jihar Kano da suke sarrafa kayayyaki daban-daban.

Sai dai abin takaici yanzu haka kamfanonin da suke aiki ka’in-da- na’in a jihar ba su wuce 20 ba. Hakan ya yi sanadiyyar asarar dubban ayyukan yi wadanda a baya matasa da magidanta ke samun na rufa wa kai aisiri.

A tattaunawarsa da Aminiya, Mataimakin Shugaban Gamayyar Kungiyar ’Yan Kasuwa, Masana’antu, Ma’adinai da Harkokin Noma ta Jihar Kano (KACCIMA), Ambasada Usman Darma, ya koka cewa baya ga wadannan kamfanoni da yawansu bai wuce 20 ba, ragowar masana’antun da suke aiki kusan dukkansu ana sarrafa shinkafa ce.

“Wadannan kamfanoni su kuma da kake gani, yawancinsu manufofin gwamnati ne suka kafa su. Daga lokacin da kuma wadannan manufofin na gwamnati suka ja baya ko aka samu canjin gwamnatin da alkiblarta ba a nan bangaren yake ba, to za su iya durkushewa,” inji Ambasada Usman.

Mataimakin shugaban Kungiyar KACCIMA, Ambasada Usman Darma

Ambasada Darma ya ce yawancin waxannan masana’antu na shinkafa gwamnati ce ta ba su jari, ko da dai ya ce duk da haka kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, kasancewar har yanzu farashin shinkafar sai kara tashin gwauron zabo yake yi.

A ina gizo ke sakar?

Da ya juya kan dalilin da ya jawo rufe mafi yawan masana’antun na Kano, Ambasada Usman ya alakanta matsalar wutar lantarki da rashin tallafin gwamnati a matsayin abubuwan da suke kara ta’azzara koma bayan masana’antun.

Ya zargi Gwamnatin Tarayya da nuna halin ko-in-kula kan harkar masana’antun a Arewacin Najeriya musamman a Jihar Kano, yana mai zargin cewa akasarin manufofin Gwamnatin Tarayya ana yi nsu ne domin su daxaxa wa Kudu.

Ya ce, “A Jihar Kano gaskiya ba a yi mana adalci. Bankunan kasuwanci da suke Kano alal misali ba sa bai wa ’yan Kano bashi da takardun Kano, sai dai na Abuja, Legas ko na Fatakwal.

“Bugu da kari, kuxin ruwan da ake sakawa ya yi yawa domin ba abin da zai taimaki dan kasuwa ba ne. Babu wani bankin kasuwanci da zai ba ka rance da kudin ruwa qasa da kashi 18 cikin 100.

“Su kuma bankunan gwamnati kamar Bankin Masana’antu da Bankin Nexim ka’idojin samun bashinsu sun yi yawa, su kuma mutanenmu ba sa iya cimma waxannan sharuxan nasu. Wannan fa ba wai Kano kawai ya shafa ba. “Amma in ka dubi Kudancin Najeriya musamman Jihar Ogun alal misali, shekara 15 zuwa 20 ba ta da masana’anta 50. Amma yanzu sun haura 1,000 saboda manufofin gwamnati suna taimaka musu,” inji shi.

Ga dukkan wanda ya san rukunin masana’antu na unguwannin Sharada da Bompai da Challawa da Tokarawa, yawancin kamfanonin da a da suke aiki yanzu sun zama kufai saboda dalilai da dama.

Yayin da wasu daga cikinsu suka rufe tare da qaura zuwa sassan Kudancin Najeriya, wasu kuma da dama sun rufe gaba daya sakamakon durkushewar da suka yi. Ko a ’yan shekarun bayan nan, an ga kamfanoni da dama, ciki har da na BUA, mallakin Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi’u sun kaura zuwa Kudancin Najeriya.

Yawancinsu dai na cewa harkar tafiyar da masana’antun takan fi tsada ce a Kano saboda qarancin wutar lantarki, wanda hakan ya tilasta musu amfani da man dizal da shi kuma tsadarsa ba za ta bar su su samu wata riba ta ku zo ku gani ba.

Masana’antun da suke tashe yanzu a Kano

Bincikken Aminiya ya gano cewa manyan masana’antun da suke tashe yanzu kuma suke aiki yadda ya kamata in aka cire na sarrafa shinkafa ba su wuce biyar ba. Masana’antun sun hada da Kamfanin Gongoni da Holborn da rukunin kamfanonin takalma da robobi na dan qasar China, Mista Lee, sai Kamfanin Mai na Ammasco sai kuma na sarrafa sabulai da garin sabulun wanki na Aspira.

To sai dai binciken Aminiya ya gano cewa kusan dukkan wadannan manyan kamfanoni biyar babu na dan asalin Jihar Kano ko ma dan Najeriya. Yawancin kamfanonin na ’yan kasashen waje ne.

A shekarun baya dai Kano ta shahara musamman wajen kamfanonin saka masaku inda dubbban mutane ke samun ayyukan yi.

‘Abin da ya kamata a yi don farfado da masana’antun’

A cewar Ambasada Usman Darma, muddin ana son farfado da harkar masana’antu a Kano da qasa baki daya, ya zama wajibi gwamnati ta yi tsarin da za a tayar da masana’antun da suka durqushe.

Ya ce galibi mutuwa ko durqushewar masana’antun tana da alaqa da rashin tsayayiyyar wutar lantarki da kuma rashin tallafi ko rance ga kanana da matsakaitan masana’antu.

Ambasada Darma ya ce tun tale-tale, Kano ita ce cibiyar kasuwanci a Najeriya, yana mai cewa dukkan sauran kasuwannin kasar da ita suka dogara kasancewarta kasuwar duniya.

“Kamata ya yi a ce an zo an tsaya an yi tsari yadda za a ce Kano na da dubban masana’antu. Za ka iya kirkirar kanana ko matsakaitan masana’antu kamar 2,000 a Kano cikin shekara biyu muddin akwai yanayi mai kyau saboda akwai jama’ar da za su sayi kayan,” inji Ambasada Darma.

Ya ce matukar aka farfado da masana’antun, akwai yiwuwar raguwar aikata laifuffuka da kimanin kashi 60 cikin 100. Hakan a cewarsa zai taimaka wa gwamnati musamman ta hanyar yin amfani da kudaden da take kashewa a kan harkar tsaro ga sauran muhimman ayyukan raya kasa.