✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da na aurar da ’yata da marayu 13 —Sanata Marafa

A ranar Asabar ta makon jiya ce Sanata Kabiru Marafa ya aurar da ’yarsa A’isha Kabiru Marafa tare da wadansu ’yan mata marayu 13 a…

A ranar Asabar ta makon jiya ce Sanata Kabiru Marafa ya aurar da ’yarsa A’isha Kabiru Marafa tare da wadansu ’yan mata marayu 13 a Kaduna.

Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan daura auren, Sanata Kabiru Marafa, ya ce ya dauki nauyin aurar da marayun ne saboda ba su da iyaye da za su taimaka wajen saya musu kayan aure.

“A yanzu haka akwai marayu da yawa da aka kashe wa iyaye a Zamfara kuma akwai mata da yawa da aka mayar zaurawa a jihar saboda ayyukan ’yan ta’adda.

“Wannan na daga cikin dalilan da na ga ya dace in yi abin da na yi domin na lura yaran nan sun isa aure amma sauran danginsu ko tsintsiya ba za su iya saya musu ba.

“Kuma idan yarinya ta isa aure kuma tana son aure amma ba a yi mata ba, tana iya shiga wani hali marar kyau. Saboda haka na ga ya dace in aurar da su,” inji shi.

Ya yi kira ga Shugaban Kasa ya samar da hanyoyin da za a taimaka wa Jihar Zamfara musamman wadanda ayyukan ’yan ta’adda ya shafa.

Shi ma da yake jawabi kafin daura auren, Limamin Masallacin Sheikh Tukur Adam Almannar ya yaba wa Sanata Marafa bisa daukar nauyin aurar da marayu da ya yi.

Ya ce akwai bukatar masu kudi da masu rike da madafun iko su rika taimaka wa marayu don samun babban lada a wurin Allah.

“Sanata Kabiru Marafa ya kyauta da ya aurar da ’yarsa A’isha ga Al’amin Ilyasu Abdullahi wanda ya biya Naira dubu 100 a matsayin sadakinta.”

“Sannan kuma Sanata nya dauki nauyin sauran yara 13 inda ya yi musu duk wani abu da mahaifi zai yi wa ’yarsa. Muna fata Allah Ya saka masa da alheri,” inji shi.

Ya bayyana muhimmancin taimaka wa marayu inda ya ce Manzon Allah yana kwadaitar da Masulmi su rika taimaka wa marayu da ke cikinsu.

Sheikh Tukur Almannar ya kuma yi addu’ar Allah Ya kawo karshen ayyukan ta’addanci a jihohin Zamfara da Sakkwato da Katsina da  Najeriya baki daya.

’Yan matan 13 marayu ne daga cikin wadanda ’yan ta’addan Jihar Zamfara suka kashe wa iyaye a kananan hukumomi daban-daban da ke jihar.

Bikin ya samu halartar manyan ’yan siyasa daga Jihar Zamfara da wasu jihohin Arewa. An kuma daura auren ne a Masallacin Juma’a na Almannar da ke Kaduna.

Wadansu daga cikin manyan bakin da suka  halarci daurin auren sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Mamuda Shinkafi.

Sauran sun hada da tsohon Gwamnan jihar Kaduna Sanata Ahmed Makarfi da sanatoci masu ci da kuma wadanda suka sauka.