✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da sabbin takardun Naira ba za su wadata ba —CBN

CBN ba shi da halin buga sabbin takardun kudin.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya fayyace dalilin da ya kawo musu tsaiko na wadata kasar nan da sabbin takardun Naira da aka sauyawa fasali.

A cewarsa, a halin yanzu Babban Bankin ba shi da halin buga sabbin takardun kudin da za su wadata kasar saboda takardun da ake buga kudin da su sun yanke.

Emefiele ya yi wannan furuci ne a ranar Juma’a yayin da yake yi wa Majalisar Koli ta Najeriya jawabi kan batun sauya fasalin takardun naira.

Wata majiyar Jaridar Premium Times da ta halarci zaman Majalisar ta ruwaito cewa, Emefiele ya koka kan yadda yankewar takardun da ake buga gari ko tsabar kudin suka kawo wa sabon tsarin cikas.

Emefiele ya shaida wa Majalisar Kolin cewa Kamfanin Buga Tsabar Kudi na Kasa wato Nigerian Security Printing and Minting Plc, ya gamu da wannan tasgaro na rashin takardun buga kudi, dalilin ke nan da ya hana a samu wadatar sabbin takardun N200, da N500 da kuma N1000 da aka sauyawa fasali.

“A halin yanzu takardun buga kudin sun kare wa Kamfanin balle a buga ’yan Naira 500 da Naira 1000 da za su wadata kasar.

“Sun bayar da odar kawo musu takardun daga wani kamfani a Jamus da kuma wani kamfani mai suna De La Rue da ke Birtaniya, amma har yanzu zaman jiran tsammani ake yi.

Ya kara da cewa, “mun mika wa Kamfanin bukatar buga sabbin takardun kudi miliyan 70, wanda hakan zai sa a samu karin Naira biliyan 126 zuwa yau (Juma’a) suna yawo a tsakanin al’umma, amma hakan bai samu ba saboda yankewar takardun.

Bayanai sun ce Shugaba Muhammadu Buhari wanda bai yi wani dogon jawabi ba a zaman majalisar, ya fice daga taron yayin da lokacin sallar Juma’a ya karato, inda mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ci gaba da jagorantar taron.