✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da Tinubu ya tafi ziyara kasashe uku

Buhari ma dai na yawan tafiye-tafiyen ganin likita a ketare.

Zababben shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya musanta rahotannin da ake yadawa cewa ba ya da koshin lafiya.

A wata sanarwa da kwamitin yakin neman zabensa ya fitar, ya bayyana cewa Tinubun ya ziyarci wajen Najeriyar ne domin ya huta tsananin gajiyar yakin neman zabe ta yadda zai kintsa wa karbar mulki.

An dai ruwaito cewa da siyasar ya fice daga Najeriya a Talatar wannan mako, inda zai ziyarci Landan daga nan ya wuce birnin Paris na Faransa kana ya yada zango a Saudiyya domin sauke farali na Umrah gabanin dawowa kasar.

‘Yan Najeriyar da dama dai na maida hankali kan lafiyar Bola Tinubu a kasar da a baya aka samu shugaban da ya rasu bayan fama da rashin lafiya mai tsawo.

Shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari ma dai na yawan tafiye-tafiyen ganin likita a ketare, inda a farkon shekarar 2017 ma ya yi zaman watanni uku a Birtaniya a kan cutar da ba a bayyana ba.

Zababben shugaban na Najeriya dai ya yi ta fitowa a wasu hotunan bidiyo babu karsashi lokacin yakin neman zabensa inda kalamansa da ma yanayin kuzarinsa ke nuna yadda karfi ke kare masa.

A halin yanzu ma dai manyan ‘yan takarar shugabancin kasar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour, na kalubalantar nasarar Bola Tinubu a kotu.