✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa muka kama gandaye 11 a Kano —Hisbah

Ya ce hakan dai ya saba da koyarwar addinin Musulunci.

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama mutane 11 da suka hada da mata takwas da maza uku saboda laifin cin abinci da rana tsaka a watan Ramadan a jihar.

An dai kama su ne yayin wani samame da dakarun hukumar suka kai unguwannin Sharada da Tudun Murtala dake Kananan Hukumomin Birni da kewaye da kuma Nassarawa a jihar.

Mai rikon mukamin shugabancin hukumar, Dakta Musa kibiya ya ce hukumar ta yi kamen ne bayan samun wasu bayanan sirri daga mazauna yankunan a lokuta daban-daban.

“Mazauna unguwannin ne suka ba mu bayanai, inda muka je Tudun Murtala muka kama mata biyar da maza uku suna cin abinci kiri-kiri da ranar Allah.

“A Sharada kuwa, mun kama mata ne guda uku,” inji shi.

Ya ce hakan dai ya saba da koyarwar addinin Musulunci.

To sai dai wadanda aka kama din sun musanta aikata laifukan da ake zargin su da yi, inda suka ce suna da hujja.

’Yan matan dai sun ce ba sa yin azumin ne saboda suna cikin jini, yanayin da a cewarsu ba zai yuwu su yi azumi a ciki ba.

Dakta Kibiya ya ce hukumar za ta gudanar da zuzzurfan bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Ya kara da cewa hukumar ta Hisbah ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen shiga dukkan lungu da sakon jihar domin kama gandayen.