✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa ’yan bindiga suke hakon Kaduna – El-Rufa’i

Gwamnan ya kuma kwatanta masu yunkurin tattaunawa da ’yan bindigar da masu karancin tunani.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya ce ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane na hakon jiharsa ne saboda matsayin da gwamnatinsa ta dauka na kin tattaunawa da su.

Ya fadi haka ne a cikin shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels ranar Lahadi, inda ya sake nanata cewa har yanzu yana nan a kan bakansa kuma ba zai bayar da kai bori ya hau ba kan tattaunawar.

Ya ce, “Ina tunanin dukkan ’yan bindiga da shugabanninsu sun yanke shawarar yin sansani ne a Kaduna saboda matsayin da muka dauka cewa ba za mu tattauna da su ba, ba za mu basu ko sisi ba daga lalitar al’umma.

“Kuma duk wanda ya san ya zo Kaduna ne da niyyar aikin ta’addanci ko garkuwa da mutane akwai yiwuwar ya rasa rayuwarsa”.

Gwamnan ya kuma bayyana masu yunkurin tattaunawa da ’yan bindigar a matsayin masu karancin tunani.

“Mun yi amannar cewar mafita a wannan matsalar ita ce mu dada tsaurara matakan tsaro ta sama da kasa har sai mun ga bayansu, babu wani dan ta’adda da ya kamata ya ci gaba da rayuwa,” inji shi.

El-Rufa’i ya ce zabin da kawai ya ragewa duk al’ummar da ta san abinda take yi shine ta yi amfani da karfin tuwo kan irin wadannan bata-garin, yana mai cewa ba za su zuba ido a rika yin fito-na-fito da gwamnati ba.

“Idan ka kakkabe kamar kaso 95 cikin 100 daga cikinsu kaso biyar kuma suka nuna a shirye suke da su tuba su rungumi zaman lafiya za mu iya yin haka, amma ba zai yuwu a tashin farko mu fara tattaunawa da su ba.

“Babu inda ake zama a tattauna da ’yan ta’adda a duniya, in ka yi haka kamar kana kara musu karfi ne,” inji Gwamnan.

Game da dalibai 39 da aka sace Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya dake Afaka a jihar ranar 11 ga watan Mayun 2021 kuwa, El-Rufa’i ya ce gwamnatinsa na yin amfani da fasaha da jami’an tsaro wajen gano maboyar masu garkuwa da daliban don ganin an kubutar da su.