✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Daminar bana: Cibiyar bincike ta shawarci manoma su fara shuka da wuri

Daminar bana: Cibiyar bincike ta shawarci manoma su fara shuka da wuri

Cibiyar Bincike kan Ayyukan gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (IAR) ta shawarci manoma da su yi shuka a kan lokaci sannan su yi yi amfani da ingantaccen iri a daminar bana.

Daraktan cibiyar, Farfesa Muhammad Faguji Ishiyaku, ne ya bayar da shawarar a tattaunawarsa da Aminiya a Zariya ranar Laraba.

Ya ce sun bayar da shawarar ce bisa hasashen Hukumar Kula da Yanayj ta Najeriya (NiMET) ta bayar na yiwuwar samun ruwan sama da wuri.

Farfesa Muhammad ya kuma shawarci manoma da su sami ingantattun iri domin kauce wa yin hasarar amfanin gonna.

Masanin ya ce zai yi kyau manoma su shuka sabbin irin wake da gyada da dawa da masara masu jurewa fari ko da ya auku.

Haka kuma ya shawarci manoma da su rungumi amfani da kayan aikin gona na zamani domin samun amfani mai yawa.

Daraktan ya bukaci manoma da su rika neman shawarar malaman gona akan abinda ba su ganeba.