Daily Trust Aminiya - Dan sanda ya harbe dan Acaba kan N50
Subscribe

‘Yan Sanda

Dan sanda ya harbe dan Acaba kan N50

Rahotanni sun bayyana cewa wani dan Achaba ya rasa ransa a yayin da rikici ya kaure tsakaninsa da wani dan sanda a yankin Agodi-gate da ke birnin Ibadan a jihar Oyo.

Wani wanda ya gane wa idonsa faruwar lamarin ya shaida wa Aminiya cewa, lamarin ya faru ne a yayin da dan sandan ya nemi dan Achaban ya ba shi cin hancin N50, wanda kuma dan Achaban ya hana.

A cewarsa, dan sandan ya yi barazanar harbin dan Achaban saboda ya hana shi kudi kuma ana tsaka da haka ne dan sandan ya yi kokari zare makullin baburin, wanda hakan ya kai su ga fara kokawa.

Ana wannan hali ne dan sandan ya harba bindigarsa kuma aka yi rashin sa’a harsashin ya samu dan Achaban kuma nan take ya ce ga garinku nan.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Mai Magana da Yawun Rundunar ’Yan Sandan jihar, ASP Oduniyi Omotayo, sai dai bai daga wayarsa ba.

More Stories