✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan sanda ya mayar da N600,000 da aka tura masa bisa kuskure

Wasu 'yan sanda uku sun nuna halin kwarai a fagen aikinsu,

An samu wani dan sandan Najeriya, CSP Elemide Akinkunmi da ya mayar da N600,000 da aka tura a asusunsa na banki bisa kuskure.

Wata sanarwa da rundunar ’yan sandan ta fitar ta ce Sufeto Janar Usman Alkali Baba ya yaba wa CSP Elemide, jami’in dan sandan da ya nuna halin kwarai da ba kasafai ake samu ba yayin gudanar da aikinsu.

Za a yi itikafi bana a Masallatan Harami —Saudiyya

Dan sandan wanda shi ne shugaban gudanarwa na gidan rediyon ’yan sanda ya mayar da kudin da aka yi kuskuren tura masa zuwa ga asusun kungiyar jami’an ’yan sanda.

Sanarwar ta ce Sufeto Janar na ’yan sandan ya kuma yaba wa wani dan sanda Yahaya Ahmed na kotun shari’ar musulunci da ke Gusau a Jihar Zamfara, wanda ya ki karbar cin hancin N300,000 da wani Chukwuka Jude da aka gurfanar a kotun a ranar 18 ga Maris ya ba shi.

Yahaya Ahmed

Haka kuma, Sufeto Janar din ya yaba wa wasu jami’an ’yan sanda da wasu mutanen kirki a Jihar Legas, musamman Sajen Sampson Ekikere da ke aiki da rundunar ’yan sandan sintiri mai lamba 22 a Ikeja, wanda a ranar Asabar 19 ga watan Maris, ya tsinci alaben wani mai suna Lukman Abaja, ya bi sahu har ya gano shi ya danka masa abarsa.

Sajen Sampson Ekikere

Da wannan ne Alkali Baba ya yi kira ga manyan jami’an ’yan sanda da su rika yaba wa jami’ansu da suka yi fice da nuna halin kwarai a fagen aikinsu, yana mai cewa hakan zai yi tasiri matuka wajen daga martabar rundunar ’yan sandan da kuma yi mata kyakkyawan fata.