✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan sanda ya mutu, wasu mutum 3 sun bace a kifewar kwale-kwale a Bayelsa

Har yanzu ba a gano abin da ya haddasa hatsarin ba.

Wani jami’in dan sanda ya rasa ransa yayin da wasu mutum uku suka bace a wani hatsarin jirgin ruwa da ke dauke da jami’an tsaro a jihar Bayelsa.

Jirgin dai na dauke da jami’an wani kamfanin sa ido na mai mai suna Darlon Security Surveillance Service ne, kuma ya kife a kogin Odewari da ke kusa da mahadar Korokorosei a Kudancin Ijaw da ke Jihar ta Bayelsa.

A cewar wani mazaunin yankin, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba, a lokacin da ‘yan sandan da farar hula na kamfanin ke sintiri a bakin kogin.

Ya ce jirgin ya nufi Korokorosei ne a lokacin da lamarin ya faru.

Tuni dai aka gano gawar dan sandan da ya mutu yayin da sauran kuma har yanzu ake ci gaba da lalubensu.

Aminiya ta gano cewa dan sandan ya yi ta yin ninkaya zuwa gabar kogin amma ya rasu kafin a isa asibitin Olugbobiri don ba shi agajin gaggawa.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, SP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jami’insu guda ya rasu, yayin da uku kuma ba a gansu ba.

Ya ce: “A ranar 25 ga watan Yulin 2022, wani jirgin ruwa dauke da ‘yan sanda da ke sa ido ya kife a hanyar ruwan Korokorosei, a Karamar Hukumar Ijaw ta Kudu. An tsinto gawar dan sanda daya yayin da mutum uku suka bace.

“Har yanzu ba a gano musababbin faruwar lamarin ba. An tura masu jami’ai zuwa yankin domin ceto mutanen da suka bata.” Inji shi.