✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan shekara 75 ya yi wa ’yar shekara 4 fyade

’Yan sanda sun cika hannu da wani tsoho mai shekara 75 da ya yi wa ’yar dan uwansa mai shekara hudu fyade a Jihar Nasarawa.

’Yan sanda sun cika hannu da wani tsoho mai shekara 75 da ya yi wa ’yar dan uwansa mai shekara hudu fyade a Jihar Nasarawa.

Tsohon ya yi wa kankanuwar yarinyar aika-aikan ne bayan ya yaudareta zuwa dakinsa a unguwar Daddare da ke Karamar Hukumar Obi ta jihar.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, DSP Nansel Rahman, ta wata sanarwa a ranar Lahadi ya ce babban ofishinsu da ke Kamamar Hukuamr Obi ne ya cafke tsohon ranar Asabar da safe, “bayan rahoton da aka kai wa ofishin.”

Ya ce bincikensu ya gano tsohon Najadun yana zaune gida daya ne da mahaifan yarinyar, kuma bayan an kai ta asibiti likitoci sun tabbatar cewa ya keta matuncinta.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Maiyaki Mohammed-Baba, ya ba da umarnin zurfafa bincike kan lamarin da kuma gurfanar da tsohon a gaban kuliya.