✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dangote ya kaddamar da rabon kayan abinci ga mutum 120,000 a Kano

Dangote ya bukaci sauran masu hannu da shuni su taimaka wajen ciyar da jihar gaba.

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya kaddamar da rabon tallafin kayan abinci da za a raba wa mutum 120,000 a Jihar Kano.

Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga wadanda za su jagoranci rabon kayan abinci da su tabbatar kayan sun isa ga wadanda aka bayar da tallafin domin su.

Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin da ya jagoranci kaddamar da rabon tallafin kayan abincin da Gidauniyar Aliko Dangote ta bayar don tallafa wa mabukata a jihar.

Ya kuma yaba da manyan ayyukan da Gidauniyar Dangote ke yi a Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da kuma ayyukan ci gaba da akeyi a Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil.

A jawabinsa, Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewar tallafin abinci ba iya Jihar Kano zai tsaya ba, har da sauran jihohi 36.

A cewarsa za a kuma a raba buhunam shinkafa miliyan daya a fadin kasar nan, inda Jihar Kano za ta amfana da buhu 120,000, wanda za a raba wa mabukata.

Dangote, ya bayyana cewar gidauniyarsa na gab da kammala aikin da ta fara a Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke jihar.

Ya kuma gode wa gwamnan jihar, kan irin ayyukan da yake gudanarwa.

A gefe guda kuma, ya ja hankali ga mawadata da su hada hannu wajen ciyar da jihar gaba da kuma tallafa wa mabukata musamman a wannan wata mai alfarma.

Wani magidanci da ya amfana da tallafin kayan abincin, ya yaba wa gidauniyar kan tallafin, wanda ya ce zai taimaka masa shi da iyalinsa a wannan lokaci da ake fama da tsadar rayuwa.