✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dattawan Arewa sun bukaci a hukunta sojojin da suka kai harin bom a Kaduna

Kungiyar ta ce dole a yi adalci ta hanyar wadanda ke da hannu a kai harin.

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bayyana cewa harin bam da sojoji suka kai yankin Tundun Biri a Jihar Kaduna wani lamari ne mai firgirtarwa kuma dole a dauki mataki.

Kungiyar ta bukaci a gudanar da cikakken bincike kan lamarin da ya yi sanadin salwantar rayukan masu taron Maulidi sama da 85.

Daraktan Yada Labarai na NEF, Malam Abdul-Azeez Suleiman, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce dattawan sun bukaci Gwamnatin Jihar Kaduna ta tashi tsaye wajen gudanar da bincike tare da tabbatar da an biya diyya ga wadanda lamarin ya shafa.

“Baicib biyan diyya ga wadanda abin ya shafa, cikakken bincike yana da matukar muhimmanci don tabbatar da adalci, tare da hana aukuwar irin haka a nan gaba, da kuma kiyaye ka’idojin kare hakkin bil Adama da dokokin jin-kai na kasa da kasa.

“Ta hanyar gano musabbabin faruwar lamarin da kuma yanayin da ke tattare da lamarin, binciken zai iya tantance ko wane irin sakaci ne ya faru, tare da hukunta wadanda ke da hannu a lamarin.

“Wannan zai samar da diyya, tare da karfafa amincewa tsakanin sojoji da farar hula,” in ji Suleiman.

Ya ce gudanar da cikakken bincike kan harin bam din na da matukar muhimmanci don hana aukuwar irin wannan lamari a nan gaba.

“Wadannan matakan za su rage hatsarin tashin bama-bamai da kuma kare rayukan fararen hula yayin ayyukan soji. Bincike ya yi daidai da ka’idodin ’yancin dan Adam da dokokin jin-kai na duniya.

“NEF na jajanta wa iyalan wadanda lamarin ya shafa da kuma Gwamnatin Jihar Kaduna bisa wannan mummunan lamari,” in ji Suleiman.