Daily Trust Aminiya - Dattawan Arewa sun yi tir da masu goyon bayan hafsoshin tsar
Subscribe

Dattawan Arewa sun yi tir da masu goyon bayan hafsoshin tsaro

Kungiyar Dattawan Arewa ta yi tir da kungiyoyi masu zaman kansu da ke goyon bayan a bar hafsoshin tsaron Najeriya a kan kujerunsu.

Hakan ya biyo bayan sukar da wasu kungiyoyi 16 mazauna Legas suka yi wa dattawan Arewan saboda kiran da suka yi wa Shugaba Buhari ya sauke manyan hafsoshin tsaron.

Kungiyoyin sun kalubalanci dattawan ta hanyar bayyana gudunmawa da hafsoshin ke bayarwa wajen magance matsalar tsaro a kasar.

Sai dai Gamayyar Kungiyar Dattawan Arewan ta CNEPD a ranar Litinin ta bayyana matsayin wadancan kungiyoyi da cewa cin mutunci ne ga ’yan Najeriya, duba da irin matsanancin hali da ake ciki na matsalar tsaro, wanda a kullum kashe mutane ake yi musamman a yankin na Arewa.

Jawabin CNEPD dauke da sa hannun Shugabanta, Injiniya Zanna Goni, ya ce wancan ikirari na cewa cire hafsoshin zai kawo koma baya ga harkar tsaro a ba gaskiya bane.

“Mun abun da muke fada, saboda mu ne ke zaune a Arewa maso Gabashin kasar nan saboda dukkanin kungiyoyin da suke goyon bayan hafsoshin a Legas suke da zama kuma basu san wane irin hali mazauna wannan yanki suke ciki ba”.

“Muna da labarin biyan su aka yi su fitar da wancan jawabi nasu domin kawo nakasu ga shirin kungiyar dattawan Arewa na ganin Shugaban Buhari ya saurari kokenmu na kawo dauki ga wannan yanki”, a cewar Goni.

Ya kara da cewa hafsoshin ba sa ba wa Shugaban Kasa bayanan gaskiya dangane da harkar da ta shafi matsalar tsaro.

A cewarsa daga cikin manyan matsalolin tsaron har da yadda ‘yan Boko Haram suka kai wa Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum hari sau uku a cikin kasa da wata uku.

“Mutane da dama ba za su iya komawa muhallansu ba saboda halin rashin tsaro da ake fama da shi a Arewa.

“Ba muna magana a kan Legas ba ne, muna magana ne a kan abin da ya shafi Arewa wanda yake cike da matsalolin tsaro.

“Da a ce hafsoshin suna yin abin da ya kamata a kan harkar tsaro, ina da tabbacin babu wanda zai bukaci lallai sai an sauke su”, inji Goni.

More Stories