✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daurawa ya shiga ofis bayan dawowarsa Hisbah

Karon farko ke nan da mashahurin malamin ya shiga harabar ofishin hukumar tun da ya sanar da murabus dinsa a ranar Juma'a

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya isa ofishinsa a karon farko bayan ya dawo bakin aiki.

Karon farko ke nan da mashahurin malamin ya shiga harabar ofishin hukumar tun da ya sanar da murabus dinsa a ranar Juma’a kan sukar da Gwamna Abba Kabir ya yi wa salon kamen hukumar a aikinta na yaki da masu badala a jihar.

Murabus din malamin ya bar baya da kura inda yi ta ba shi baki, gwamnatin jihar kuma ta shiga bikon sa.

A karshe ranar Litinin da dare aka shawo kansa a wani taron sirri da Zauren Malaman Kano ya jagoranta a gidan gwamnatin jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa dawowar Daurawa kan kujerarsa ke da wuya ya ba wa masu aikata badala a jihar da su tuba ko kuma su gamu da fushin hukumar.