✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Deontay Wilder da Anthony Joshua za su fafata damben boksin na Naira biliyan 80

Bayan doke Luis Ortiz a ranar 3 ga Maris, zakaran damben boksin na ajin masu nauyi na Hukumar Damben Boksin ta Duniya, Deontay Wilder, yana…

Bayan doke Luis Ortiz a ranar 3 ga Maris, zakaran damben boksin na ajin masu nauyi na Hukumar Damben Boksin ta Duniya, Deontay Wilder, yana sa ran fafatawa da takwaransa mai rike kambin boksin na duniya na kungiyar Boksin ta Duniya  (WBA) da kuma na Hukumar Boksin ta kasa da- kasa (IBF), Anthony Joshua dan asalin Najeriya.

Abin da kawai ake jira shi ne fafatawar da Joshua da Joseph Parker da ke rike da kambin Hukumar Boksin ta Duniya ta (WBO) za su yi a ranar 31 ga Maris din nan, inda da zarar Joshua ya samu nasara,  zai fafata da Ba’amurken,  Wilder.

Wannan yana nufin a karon farko a tarihin wannan rukuni, dukan manyan kambi hudu na duniya na – WBC da WBA da IBFda kuma WBO – za su kasance a kasuwa.

Wakilin Joshua, Eddie Hearn, wanda yanzu shi ne wanda ya fi karfafa harkar damben boksin a Birtaniya ya shaida wa kafar labarai ta CBS Sports cewa daga “dukan alamu” Wilder da Joshua za su gwabza a bana.

Kuma idan kudin da aka sanya zai kai rubu’in biliyan daya na Dala (Fam miliyan 180) kamar yadda tsohon zakaran damben boksin na duniya Ebander Holyfield ya ce sun kai, to Joshua ne zai cinye kudin ya kai gidansa.

Ya ce, dabarun Deontay Wilder ababen tuhuma ne, “Eh, Wilder ya doke wadansu abokan karawansa har sun fadi kasa sumammu. Kuma Wilder yana da tarihin lashe wasa 40, (39 a bugun tashi ka sha gari). Amma duk da nasarorinsa har yanzu yana kokarin yadda zai samu nasara ce a kan gogaggun ’yan damben boksin.

Zakaran matsakaicin aji na duniya, Billy Joe Saunders ya fadi a shafinsa na tweeter cewa dan damben mai shekara 32 zai yi wuya ya juri gwada kwanji da Joshua, bayan ya kalli yadda Ba’amurken ya sha wahala kafin samun nasara a kan Ortiz.

Wakilin wasannin damben boksin na jaridar The Guardian, Kebin Mitchell ya ce Wilder “bai da kwarewa,” a fage kuma yana “rashin karfin hali,” kuma “ko yaya ne za a gan shi kwance a kasa… yayin da Joshua ke tsaye a kansa.”

Hatta masu nazari daga Amurkawa suna ganin Joshua zai doke Wilder. Misali tsohon mai horar da Mike Tyson,Teddy Atlas, wanda ke bayar da labaran boksin ga tashar ESPN, ya shaida wa manema labarai a bara cewa “Wilder ya kware wajen kai duka (amma) Joshua ya fi kwarewa wajen fada.” Ya kara da cewa: “Wilder yana da karfi – kuma shi ne jarinsa. Amma Joshua ya fi kwarewa ya fi dabaru.”

Wilder dai yakan kai duka da karfin gaske ta yadda hannunwansa suke budawa, kuma a lokacin da yake kokarin kare kansa yakan gaza, saboda hannuwansa kan cira sama ya bar daukacin fuskarsa a fili, ta yadda abokin karawarsa zai iya dukansa a fuska, inji shi.

Ya ce ginshikin farko a boksin shi ne “ka kare kanka a kowane lokaci” amma Wilder na fama da matsalar haka. Kuma idan ya bayar da irin wannan dama take zai hadu da dukan kwaf-daya daga kwararrun irin su Joshua, wanda ya doke bladimir Klitschko a bara.