✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Direbobi suna yajin aiki saboda ’yan bindiga a Zamfara

Sun ce matakin ya zama dole domin mahukunta su dauki mataki

Direbobin motocin haya sun fara yajin aiki domin shawo kan mahukunta su kawo karshen ayyukan fashi da sauran ta’addancin ’yan bindga a hanyar Gusau zuwa Dansadau a Jihar Zamfara.

Direbobin sun koka da cewa kisan kai da sauran barnar da ’yan bindiga ke yi ya zama ruwan dare a hanyar mai tsawon kilomita 100, don haka wajibi ne mahukunta su yi su wa tufkar hanci.

Shugaban kungiyar direbobi ta NURTW reshen Jihar, Isihu Ticha “Ko ranar Juma’a sai da aka harbe direban wata motar da ta dauko amarya da a kusa da kauyen Mashayar Zaki, wanda ya yi kaurin suna wajen ayyukan maharan. Sai da motar da yi kundunbala, amma hakan bai hana maharan yin garkuwa da fasinjojin ba.”

“Kafin nan an kashe direbobi uku, wasu hudu kuma aka yi garkuwa da su, kuma yanzu akalla kwana 40 ba a sako su ba.

“Masu garkuwar na neman kudin fansa, kuma ba mu da tabbacin ko direbobin suna raye, gaskiya muna cikin mawuyacin hali,” inji shi.

Ya ce duk da cewa an girke sojoji a kan hanyar, adadinsu zai iya dakile dakile ayyukan miyagun. “Muna rokon gwamnati ta kara yawan shingayen bincike, musamman a wuraren da suka fi hadari.”

Wani mazaunin Dansadau, Alhaji Bilyaminu, ya ce direbobi kan dauko fasinjoji har zuwa Yar Tasha Sahabi, mai nisan kilomita 75 daga Gusau, amma daga nan sai su ce ba za su iya sayar da ransu su karasa da fasinja zuwa Dansadau ba.

Sai dai kakakin ’yan sandan Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu ya ce suna iya kokarinsu wajen hana miyagun motsi, sannan ya yi kira ga al’umma da su rika taimakawa da bayanan motsin bata-garin.