✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dogo Gide na neman N100m kan Daliban FGC Birnin Yauri

Dan ta’addan ya shardanta biyan Naira miliyan 100 duk da iyayen yaran sun bi ta hannun mahaifiyarsa

Iyayen daliban da aka sace a Sakandaren Gwamnatin Tarayya (FGC) ta Birnin Yauri a Jihar Kebbi na neman agaji, bayan dan ta’addan da ya sace su, Dogo Gide, ya sa musu kudin fansa Naira miliyan 100.

Dogo Gide ya sanya sharadin biyan Naira miliyan 100 ne duk da iyayen yaran sun bi ta hannun mahaifiyarsa ta matsa masa lamba ya sako ragowar ’yan mata 11 da ke hannusa kusan tsawon shekara biyu.

“Mun yi magana da Dogon Gide ranar 15 ga wagan Disamba, 2022, da farko ya ki magana, amma bayan mahaifiyarsa ta sa baki, ya amince zai sako yaranmu idan mun biya Naira miliyan 1oo, ko kuma mu hakura da su.

“Ya fada karara cewa idan ba mu yi abin da ya ce ba, har abada ba za mu sake jin duriyar ’ya’yanmu ba,” in ji Shugaban kungiyar iyayen daliban, Salim Kaoje.

Ya bayyana haka ne a wani taro da suka yi a makarantar a ranar Lahadi, inda suka ce sun riga sun ga gazawar gwamnati wajen ceto musu ’ya’ya, don haka ba su da zabi face yin abin da suke ganin za su iya.

Kusan shekara biyu ke nan, a watan Yunin 21, ’yan bindiga suka kai hari Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya ta Birnin Yauri suka yi awon gaba da dalibai 80, kuma har yanzu suna tsare da 11 daga cikin yaran.

Kaoje ya ce hakan ne ya susuke karo-karo daga hannun jama’a don tara kudaden da dan ta’addan ya shardanta, “shi ya sa muka zo domin yin wannan roko.”

Kaoje ya ce kowanne daga cikin iyayen daliban ya amince ya sayar da duk kadarorinsa domin su hada kudaden.

Mahaifin daga cikin daliban, Umar Abdulhamid, ya ce ba su da zabi saboda sun riga sun yanke kauna daga gwamnati.

Ya ce, “Kusan shekara daya da wata takwas ke nan da aka sace mana ’ya’ya; mun jira gwamnati, ba ta da shirin ceto su.”

Mahaifiyar daya daga cikin daliban, Serah Musa, ta ce shi ya sa suke rokon jama’a su taimaka musu.

“Tun da aka sace su ba mu koma hayyacinmu ba, mun yi kuka har hawayenmu ya bushe, kananan yara ne bai kamata a bar su hannun ’yan ta’dda ab, babbarsu shekarunta 16.”

Don haka ta roki jama’a da su kawo musu dauki a hada kudaden domin ceto rayuwar yaran.