✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar haramta wa dalibai sanya nikabi a Masar ta janyo ce-ce-kuce

Gwamnatin kasar Masar ta dage kan cewa haramta wa dalibai Musulmi sanya nikabi wata hanya ce ta rage tsattsauran ra’ayin addinin Islama

Dokar haramta amfani da nikabi ko kuma kyallen rufe fuska ga mata a cikin makarantu ya haifar da ce-ce-ku-ce a kasar Masar tun bayan da ma’aikatar ilimin kasar ta sanar da matakin.

A safiyar ranar Litinin ne jaridu da kuma kafofin yada labaran kasar suka wayi gari da bai wa jama’a labarin sanarwar gwamnati na haramta wa dalibai mata amfani da Nikabi a cikin makarantun firamare da sakandare.

Sabuwar dokar ta kuma sanya amfani da hijabi ko kuma rufe kai a matsayin zabin da dalibai ke da shi ko dai su sa ko kuma su bar shi, ko kuma idan iyayen su sun tilasta musu.

To amma da alama wannan doka ba ta yi wa jama’ar kasar da ke da rinjayen mabiya addinin Musulunci dadi ba, inda suka rika tofin ala tsine ga gwamnati musamman a shafukan su na X wato Twitter a baya.

To amma gwamnatin kasar ta dage kan cewa wannan wata hanya ce ta rage tsattsauran ra’ayin addinin Islama, abin da ya bai wa masu goyon bayan dokar ayyana duk mai yaki da ita a matsayin magoyin bayan kungiyar Taliban da kuma IS.

Duk da wannan ce-ce-ku-ce da ake yi har yanzu gwamnatin kasar ba ta ce komai game da dokar ba, abin da ke nufin ta tsaya kan matsayar ta na haramtawa ’yan matan amfani da nikabi da kuma ba su zabin rufe gashinsu ko akasin haka.

Wannan mataki dai na zuwa ne makonni biyu bayan da kotun Faransa ta tabbatar da dokar hana amfani da hijabi ko kuma duk wani na’u’i na suturta jiki da mata Musulmi ke yi a cikin makarantu.