✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole a kori hafsoshin tsaro —Dattawa Arewa

Kugiyar Dattawan Arewa ta sabunta kiranta na a yi wa tsaron Najeriya garanbawul

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta sabunta kiranta na yi wa harkar tsaron Najeriya garanbawul ta hanyar farawa da cire Manyan Hafsoshin Tsaron.

Dattawan sun ce dubban daruruwan mutane a yankin sun fada cikin mawuyacin hali sakamakon ayyukan ’yan bindiga, barayin shanu da masu garkuwa da mutane ba tare da samun kulawa daga jami’an tsaro ba.

“A bayyane yake cewa harkar tsaro a Najeriya na cike da kalubale iri-iri, matukar za a rika zargin jami’an tsaro da kisan mutane ba bisa ka’ida ba.

“Ba za mu lamunci a kyale dubban ’yan uwanmu a Arewacin Najeriya su rika fama da matsalar ’yan bindiga da masu tayar da kayar baya ba amma ’yan sanda sun rungume hannunsu ba tare da tabuka wani abin a zo ku gani ba”, inji kungiyar.

Sanarwa da Sakataren Watsa Labaranta Dokta Hakeem Baba-Ahmed ya fitar ranar Litinin ta ce ya kamata a yi amfanai da irin hobbasan da aka yi wajen yin tir da ’yan sandan SARS wajen magance matsalar tsaron da ta addabi Arewacin Najeriya.

Kungiyar ta ce duk da matakin da Shugaban Kasa ya dauka na rushe SARS da kuma bincikar wuce gona da iri da suke yi, idan aka kwatanta shi da tarin bukatun da ake da su ga shugaban, to alal hakika akwai matsala a harkar tsaron kasa.

Ta kara da cewa, “Akwai abubuwan da dama da ya kamata gwamnatocin baya da ma mai ci su bincika amma suka yi watsi da su saboda karancin yin komai ba tare da kumbiya-kumbiya ba.

“Abin takaici ne yadda gwamnati ke tunkarar matsalolin tsaron rayukan jama’arta.

“Sai da aka tilasta mata kafin ta dauki matakin baya ga tarin abubuwan da suka jawo ayar tambaya game da nagartar ’yan sanda,” inji kungiyar.