✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta sako Mailafia bayan ya amsa gayyatarta

Hukumar DSS ta sako Obadiah Mailafia bayan ya amsa gayyatarta a karo na biyu

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta sako tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Obadiah Mailafia, bayan ya sake amsa gayyatarta a karo na biyu.

Dokta Mailafia, wanda kuma tsohon dan takarar shugaban kasa ne a zaben shekara ta 2019 a karkashin jam’iyyar ADC, ya je ofishin hukumar ne da ke Jos da misalin karfe 12 na rana, daga bisani kuma aka sallame shi sa’a daya bayan zuwan nasa.

Da safiyar Litinin ne dai hukumar ta sake gayyatarsa domin ya amsa tambayoyi a karo na biyu, kamar yadda lauyansa, Yakubu Bawa, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).

Lauyan ya kuma ce sabuwar gayyatar na da nasaba da ganawar Mailafia da hukumar a makon jiya.

“Ba wani abu ba ne na daban da ganawarsa ta farko da DSS, wadda ta musayar ra’ayi ce kawai”, inji shi.

Idan ba a manta ba, ranar Larabar makon jiya ce hukumar DSS ta gayyaci Mailafia bayan wata tattanawa da ya yi da gidan rediyon Nigeria Info da ke Abuja.

Yayin tattaunawar dai Mailafia ya yi zargin cewa daya daga cikin gwamnonin arewa na mara wa Boko Haram.

Daga bisani hukumar ta saki tsohon Mataimakin Gwamnan na CBN bayan an kwashe sa’o’i shida ana yi masa tambayoyi.

Hukumar dai ta fitar da sanarwa tana cewa Dokta Mailafia ya yi nadamar abubuwan da ya fada har ya nemi afuwa, shi kuma ya ce yana nan a kan bakanshi.