✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubun ’yan bindigar da suka addabi Zariya ta cika

Sun tabbatar da hannunsu a hare-ahren da suka hana yankunan Zariya sakat.

’Yan sanda a Jihar Kaduna sun cafke mutum biyar mazauna unguwannin Zariya da ake hada kai da su ana ayyukan ta’addanci a Zariya da kewaye.

Kamun na zuwa ne mako daya bayan wasu munanan hare-hare tare da kashe mutane biyu da kuma sace wasu biyar a Zariyan.

A ranar Alhamis, 15 ga watan Yuli, 2021 ’yan sanda masu yaki da ’yan fashi da kuma satar mutane (FIB-IRT) suka kama ’yan bindigar.

Wadanda aka kama din mazaunan kauyen Kwaba da wani boka a Anguwar Juma, sai wani dan unguwar Nagoyi, da dan unguwar Dankali da kuma wani dan Tudun Wadan Zariya.

Mutanen da ake zargin sun amsa cewa su ne suka yi garkuwa da mutane a unguwannin Gwargwaje da Madaci da kuma Kofar Gayan —duk a Zariya.

Sun kuma ce su ne suka sace matar Dagacin kauyen Kwaba, Aminu Mustapha da iyalan wani mai suna Alhaji Bature, suka karbi kudin fansa Naira miliyan daya a kan kowannensu.

Mutanen da ke hannu sun tabbatar cewa su ne suka sace shanu bayan sun kai hari gidajen Malam Shage da Alhaji Mai Lema da Alhaji Bammi da kuma Alhaji Ali.

A yayin bincike an gano bindigogi AK 47 biyu kirar gida da kuma harsasai 162 da sauran makamai da kuma karfen da suke karya kofa a shi. ’Yan sanda na ci gaba da bincike kan mutanen.

Hare-haren ’yan bindiga a kwanan nan

’Yan bindiga bi-la-adadin ne suka kai hare-hare a ranakun 9 da 10 na watan Yulin da muke ciki a kananan hukumomi uku na Jihar Kaduna inda suka kashe mutum biyu, suka harbi wani, sannan suka sace wasu biyar da kuma garken shanu.

Sai kuma kauyen Dan Kunsai, da Tashar Dorawa, da kuma garin Kaya duk a gundumar Fatika a Karamar Hukumar Giwa da ke Jihar Kaduna.

“Karo na biyar ke nan da ’yan bindigar suke kawo mana hari a anguwar Kofar Gayan,” a cewar Auwal Ibrahim, wanda ’yan bindigar suka harba a yayin harin.

Ya ce bayan kwashe sa’a biyu ana artabu da su, maharan ba su samu nasara ba sakamakon daukin gaggawa da al’ummar gari da kuma hadin gwiwan jami’an ’yan sanda da kuma ’yan sa-kai.

A halin yanzu matashin mai shekara 25 yana kwance a wani asibiti a Zariya yana karbar magani.

Da misalin 11:30 na dare kuma masu garkuwa suka kai hari a kauyen Milgoma, daura da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello, inda suka fasa gidan wani Malamin Jami’ar Gwamnatin tarayya da ke Dutsinma a Jihar Katsina.

’Yan bindigar sun dauke matarsa mai suna Jummai Suleiman, ma’aikaciya a sashen kula da masu fama da lalurar kwakwalwa na asibitin da kuma ’ya’yanta uku masu shekara 10, shida da kuma hudu.

Masu garkuwar sun kuma dauke wata ma’aikaciyar Jami’ar Ahmadu Bello, a kauyen da ke daura da makarantar Zariya Academy — duk a ranar. Amma matar ta kubuta a yayin artabun da jami’an tsaro suka yi da maharan.

A wani harin na ranar 9 ga watan Yuli da misalin 12.00 na dare, mahara sun je Dan Kunsai inda suka yi awon gaba da wasu shanun huda.

’Yan bindigar sun nemi yin garkuwa da Alhaji Lawal da kuma Alhaji Bilya, amma suka turje, su kuma nan take suka bindige su.

Da misalin 12.30 na ranar Asabar 10 ga Yuli, mahara sun je kauyen Tashar Dorawa inda suka sace kusan shanu 100 mallakin Alhaji Shume.

A safiyar ranar masu garkuwa suka sace wasu mutane a garin Maska na Jihar Kastina, suka shigo da su garin Kaya inda suka sace wani mai suna Rabi’u Ishaq.