✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Duk da gargadin CBN har yanzu bankuna na bai wa mutane tsoffin kudade ta ATM

Mun ba su wadatattun sabbin kudi, babu dalilin da zai sa su hana mutane.

Rahotanni na nuna cewa har yanzu bankuna ba su fara bin umarnin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ba su ba na daina bayar da tsofaffin takardun kudi a na’urar cire kudi ta ATM ba.

A ranar Alhamis ne dai CBN din ya ce duk wanda bankin suka bai wa tsohon kudi kada ya karba, domin babu gudu ba ja da baya kan daina amfani da su daga ranar 31 ga watan Janairu.

Sai dai wakilanmu da suka ziyarci ATM din bakuna daban-daban a Jihohin Legas da Kano, da Nasarawa da Sakkwato da Adamawa ranar Alhamis, sun bayyana mana ATM da dama tsofaffin kudi suke bayarwa, wasu kuma gwamutsawa suke yi da sababbin.

Su ma ’yan kasuwa da ke sana’o’insu a Kasuwar Sabon Gari da Kwari da Wambai da Kurmi a Kano, sun bayyana damuwarsu kan yadda sababbin kudin suka yi karanci, yayin da mutane suka fara daina karbar tsofaffin kudin da ko a bankuna su ake ba su.

Shugaban kungiyar dillalan Kasuwar Sabon Gari, Alhaji Sule Umar Kura ya bukaci CBN da ya wadata bankuna da sabbin takardun kudi domin su yawaita a hannun al’umma.

Za mu dauki mataki kan bankuna —CBN

Sai dai shugaban CBN reshen Kano, Umar Ibrahim Biu, ya ce duk bankin da ya gaza bin umarnin Babban Bankin, za a sanya masa takunkumi.

Ita ma Mataimakiyar Daraktan CBN, Rekiyat Yusuf ta yi kira ga ’yan Najeriya da su dinga mayar wa bankunan tsofaffin kudin da suka ba su, domin CBN din ya ba su sababbin da za su bai wa al’umma.

“Idan bankuna suka baku tsofaffin kudi, ku mayar musu da kayansu, sannan ku kawo mana kararsu a hukumance.

“Mun ba su wadatattun sabbin kudi, babu dalilin da zai sa su hana mutane,” in ji ta.