✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk da hada layin waya da NIN garkuwa da mutane na ci gaba

Daga 16 ga Disamban 2020 zuwa Janairun 2024, akalla mutum 12 ,586 aka sace a Najeriya.

Duk da hada layin waya (SIM) da lambar Katin Dan Kasa (NIN) na ’yan Nijeriya har yanzu matsalar tsaro a sassan kasar nan na ci gaba da ta’azzara kamar yadda wannan rahoto na Aminiya ya gano.

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa rajistar da hada lambar wayarsu da ta NIN za su taimaka wa jami’an tsaro wajen kama ’yan ta’adda a kasar nan.

Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar 26 ga watan Mayun 2021 ya bayyana gamsuwarsa da cewa hada layukan waya da na NIN na da matukar amfani wajen yaki da ta’adanci.

Buhari a lokacin kaddamar da tsarin tallata amfani da kayan cikin gida da kuma tsarin lambar NIN ta kasa a Abuja a wancan lokaci ya yi kira ga ’yan Nijeriya su goyi bayan hada layukansu da NIN.

“NIN zai taimaka wajen cike wani gibi a fannin tsaro, zai kuma taimaka mana wajen sanin hakikanin bayanan ’yan Nijeriya. Za mu gano mazauna ciki a saukake har da marasa gaskiya, “ in ji shi.

Buhari ya nuna cewa wannan tsari zai taimaka wajen inganta tsaro da tattalin arzikin kasa. “NIN tsarin kati ne na zamani a fannin sadarwa.

Kuma ’yan Nijeriya da doka ta amince masu dole su mallaki lambar ta musamman.

Hakan zai ba da damar amfana da gwamnati kuma zai taimaka wa gwamnatin wajen gudanar da tsare-tsaren tattalin arzikin kasa,” in ji tsohon Shugaban Kasar.

Amma bayan shekara uku da fito da tsarin, ’yan fashin daji sun sace tare da hallaka dubban ’yan Nijeriya a sassan kasar nan.

A kusan kowane lokaci da wayar hannu ’yan ta’addar suke magana da iyalan mutanen da suka sace don karbar kudin fansa.

Alkaluman da Aminiya ta samu ta rahotanni kafafen watsa labarai na nuna cewa daga 16 ga Disamban 2020 zuwa Janairun 2024, akalla mutum 12 ,586 aka sace a jihohin kasar nan da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

A shekarar 2020 kadai mutum 2,242 aka sace, dubu 4,987 a shekarar 2021, dubu 2,076 a shekarar 2022, dubu 3,063 kuwa a shekarar 2023 sai 206 a Janairun da muke ciki.

Sannan an ruwaito cewa ’yan ta’addar sun hallaka mutum 10,012 a kasa baki daya. 837 a shekarar 2020; 4,169 a shekarar 2021; 2,310 a shekarar 2022; 2,586 a shekarar 2023 sai kuma 110 a watan Janairun 2024.

Wannan bai kunshi mutum 1,569 da aka ruwaito ’yan Boko Haram sun kashe a Arewa maso Gabas ba a wannan lokaci. 747 a shekarar 2020; 260 a shekarar 2021; 192 a shekarar 2022; 268 a shekarar 2023 sai mutum 12 a cikin wannan wata.

Binciken Aminiya ya nuna cewa akalla layukan waya miliyan 13 da ake amfani da su har yanzu ba a hada su da NIN ba.

Majiyoyinmu a Hukumar Katin Dan Kasa (NIMC) sun shaida wa daya daga cikin wakilanmu cewa akalla akwai layukan waya da ake amfani da su a Nijeriya miliyan 221 da dubu 769 da 883.

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) a watan Satumban bara ta nuna akalla layukan waya miliyan 12.3 masu su har yanzu ba su hada su da NIN ba.

“Kila alkaluman su wuce miliyan 13 a Janairun da muke ciki saboda an sayar da layukan waya masu yawa a tsakanin watan Nuwamba zuwa yanzu,” in ji majiyar.

Karuwar sace-sace da kisan mutane a kasar nan na jefa shakku a zukatan ’yan kasa a kan ko ana amfani da hada layukan waya da NIN don cim ma manufar fito da tsarin.

Tsohon Ministan Sadarwa Farfesa Isa Pantami a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadin makon jiya, ya ce rashin amfani da bayanan da ake samu ne a hada layukan waya da NIM da jami’an tsaro ba su yi yake taimakawa wajen ta’azzarar sacesace da ta’adanci a kasar nan.

Ya kuma bayyana a wani sakon yadda daya daga cikin abokansa ya taimaka wajen nemo taimakon Naira miliyan 50 daga cikin Naira miliyan 60 da ’yan bindiga suka bukata kafin su sako wasu ’yan mata ’yan uwan juna shida da mahaifinsa a Abuja.

Tsohon Ministan ya mayar da martani ne ga wani mai suna Roland Metus wanda ke kalubalantar tsohon hadimin Shugaban Kasa Buhari, Bashir Ahmad wanda ya nuna damuwarsa a kan yawaitar garkuwa da mutane da ta’adanci a kasar nan.

A martanin Farfesa Pantami ya ce “Hada layukan waya da NIN na amfani amma akwai bukatar hukumomin da alhakin yaki da ta’adanci ke rataya a wuyansu su rika amfani da ingancinsa a duk lokacin da aka aikata laifin.”

Ya ce tsarin ba shi ke da laifi ba rashin amfani da tsarin ne da hukumomin ba su yi.

Wani masanin tsaro Chukwuma Ume a tattaunawarsa da Aminiya ya ce jami’an tsaro na da damar duba NIN da kuma na’urar gano duk wanda suke son bibiyarsa.

Sai ya ce amma ’yan ta’addar suna amfani ne da wayoyin wadanda suka kama wajen neman kudin fansa.

“Abin da kawai za a iya yi shi ne a jira har sai sun shigo gari. Amma kuma suna da wayo, inda ba sa amfani da layukansu da na mutanen da suka kama suke yi.

Da zarar sun saki wanda suka kama ko sun kashe shi jami’an tsaro ba za su ci gaba da bibiyar layin wayar wanda aka sace ba. (Masu garkuwar) Suna da matukar wayo.

“Game da batun ‘mallakar layi’ -sunan fasahar- da galibi Abba Kyari (dakataccen Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda kuma tsohon Shugaban Kwamitin Kar-ta Kwana (IRT) na Sufeto Janar wanda ke fuskantar zargin safarar hodar Iblis tare da jami’ansa hudu) da ayarinsa ya sa yanzu ’yan ta’addar sun nemo wasu hanyoyin da suke riga jami’an tsaro farga.

“Kamar yadda na ce ne su ’yan ta’addan ba sa amfani da layin wayarsu bayan haka su kansu kamfanonin sadarwa ba su taimaka wa gwamnati ba hakan kila saboda ba su da kwarewa ce a kan haka.

“Idan ka lura za ka ga bayan ka yi rajista, sai kuma a bukaci ka sake komawa ka yin wani rajista hakan ya nuna cewa kamfanonin sadarwa ba su yin abin da ya kamata su yi ko kuma kawai suna yi ne saboda neman riba. Idan suka nemi matsawa kila ba za su samu sayar da layukan da yawa ba. Akwai dai batun samun riba da rashin kwarewa da kuma rashin kishin kasa a bangaren kamfanonin,” in ji shi.

Wani masanin tsaro Abdullahi Garba kira ya yi ga hukumomin da ke sa ido su mayar da hankali ta hanyar tabbatar da abin ya amfani ’yan kasa.

Ya ce a wasu kasashe ba za ka iya amfani da layukan waya ba, ba tare da ana da cikakkun bayananka ba tunda farko, amma akwai wuraren da mutane ke yin algus. Mutane ba sa yin abin da ya kamata su yi.

An gano kura-kurai masu yawa wajen yin rajistar NIN —NIMC

Darakta Janar ta Hukumar Yin Katin Dan Kasa (NIMC) Injiniya Abisoye Coker- Odusote ta fadi a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis din makon jiya ta hannun mai ba ta shawara Ayodele Babalola cewa an gano kura-kurai a lokacin daukar NIN.

Ta ce kusan dukkan rahotanni a kan kura-kurai wasu abokan huldar hukumar ne suka aikata.

Masana sun kawo mafita

Wani masani Martin Nwoha wanda ya zanta da daya daga cikin wakilanmu ya ce gwamnati ta ba kamfanonin sadarwa damar yi amfani da na’urarsu ta LIMS wajen ganowa tare da bibiyar duk wani mai laifi sannan su mika bayanan ga jami’an tsaro masu zaman kansu idan ’yan sanda ko sauran jami’an tsaro sun ki yin wani abu a kai.

Ita na’urar LIMS tana taimakawa wajen gano bayanai da kuma karfin sadarwa. Tana da amfani ga layukan waya da kuma ta hanyar saurare da ganowa tare kuma da kiyaye su. Ana iya amfani da ita wajen bibiyar kiran waya da Intanet da imel da sakon tes da sauransu.

Nwoga ya ce idan za a iya samar da wata hukuma ta gwamnati da za ta rika lura da bayanan wadanda ake zargi ’yan ta’adda ne za ta taimaka wajen magance matsalar tsaro.

Shugaban Kamfanin Madjatek, Injiniya Abdul’muizz Oyewole cewa ya yi ci gaba da fuskantar matsalar tsaro a Nijeriya duk da an hada layukan waya da NIN na sanya ayar tambayoyi da suka kamata a yi kan ingancin amfani da na’urorin zamani wajen kare al’umma.

Ya bukaci a samar da wata dama da za ta ba jami’an tsaro damar duba bayanai ta hanyar layukan waya da NIN. Ya ce za a iya magance matsalar boye bayanan mutane ta amfani da wasu hanyoyi da suka dace.

Ya ce gwamnati na iya samar da isassasun kyamarorin boye da jirage marasa matuka da ka iya tattaro bayanai a wuraren da suke da hadari don daukar matakan da suka kamata.

’Yan sanda da DSS ba su ce komai ba game da zargin kin amfani da hada layukan waya da NIN.

Kokarin jin ta bakin Hedikwatar ’Yan sanda da Hukumar DSS kan zargin kin amfani da bayanan da ake samu sakamakon hada layukan waya da NIN ya ci tura domin masu magana da yawun hukumomin ba su amsa wayoyinsu ba, sannan ba su amsa sakonnin tes da aka aika masu ba.