✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk wadanda muke bi bashi sai sun biya — MTN

MTN ya ce tangardar na’ura ya fuskanta wadda ta yi kuskuren goge basussukan abokanan huldarsa.

Kamfanin Sadarwa na MTN ya sha alwashin cewa duk wasu abokanan huldarsa da yake bi bashi su kwana da sanin cewa sai sun biya.

Kamfanin ya bayyana hakan yayin da aka wayi gari yau Asabar musamman a dandalan sada zumunta cewa ya yafe wa abokanan huldarsa basussukan da suka ci.

A cewar kamfanin na MTN, tangardar na’ura ya fuskanta wadda ta yi kuskuren goge basussukan abokanan huldarsa, kuma da zarar ya yi wa tufkar hanci bayanan bashin za su dawo.

Ya bayyana cewa matsalar na’urar da ya fuskanta ce ta sanya aka rika ganin ba daidai ba wajen neman ganin ragowar kudade da data na abokanan huldarsa.

MTN ya ce wannan dalili shi ya taka rawar da abokanan huldarsa suka rika ganin babu basussukan da ake binsu.

Aminiya ta ruwaito cewa, dandalan sada zumunta sun rikide da farin ciki a yayin da masu amfani da layin sadarwa na MTN suka yi tsammanin an sauke musu nauyin basussukan da kamfanin ke binsu.

Wannan lamari dai ya zo ne bagatatan ba tare da wata sanarwa daga kamfanin sadarwar ba.

Sai dai a cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a Yammacin wannan Asabar din, ya ce dole murna ta koma ciki domin kuwa tangardar na’ura ya fuskanta, yana mai cewa da zarar komai ya daidaita hakikanin bayanan da abokanan huldarsa suka buƙata dangane da kuɗin da ke layinsu za su bayyana babu ragi ko kari.

Saboda haka kamfanin ya ce duk wadanda yake bi bashi za su ga hakikanin bashin da ake binsu da zarar injiniyoyinsu sun kammala gyare-gyare.

Da wannan sanarwa kuma kamfanin yake bai wa abokanan huldarsa hakuri kan duk wani yanayi da matsalar ta jefa su a ciki.