✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta bayar da belin tsohon Gwaman Anambra, Obiano

Bayan kwana hudu Obiano ya kasa cika sharudan da belin da EFCC ta gindaya mishi

Hukumar Hana Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta bayar da belin Mista Willie Obiano, tsohon Gwamnan Jihar Anambra, wanda ta tsare a ranar da ya sauka daga mulki.

A safiyar Litinin Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya sanar da bayar da belin Obiano wanda ya shafe kwana hudu a tsare a ofishin hukumar kan zargin aringizon kwangila ta Naira biliyan 42.

Bawa ya bayyana cewa Mista Obiano bai kai ga cika sharudan belin da aka sanya mishi ba, don haka har yanzu yana nan a hannun hukumar ba ta sake shi ba.

Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne gabanin Babban Taron Hukumomin Yaki da Rasha a Yammacin Afirka (NACIMA).

A ranar Alhamis ne dai jami’an EFCC suka cika hannu da Mista Obiano a filin jirgi na Muratala Mohmmed da ke Legas, a yayin da yake kan hanyarsa ta ficewa daga Najeriya zuwa kasar Amurka.

An tsare tsohon gwamnan ne dai sa’o’i kadan bayan ya mika ragamar mulkin Jihar Anambra ga magajinsa, Farfesa Charles Soludo.

Bayan an yi mishi tambayoyi a ofishin hukumar da ke Legas ne aka taso keyarsa zuwa hedikwatarta da ke Abuja, aka ci gaba da titsiye shi kan zargin da yake fuskanta.