✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta gabatar da sabbin tuhume-tuhume kan Emefiele

Tuhume-tuhumen 26 sun hadar da almundahana wajen fitar da dala biliyan biyu da Emefiele ya yi ba bisa ka'ida.

Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta gabatar wa Babbar Kotun Jihar Legas, sabbin tuhume-tuhume kan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele.

Tuhume-tuhumen 26 sun hadar da almundahana wajen fitar da dala biliyan biyu da Emefiele ya yi, don taimaka wa masu canjin kudade ba bisa ka’ida ba.

Matakin EFCC  na zuwa ne daidai lokacin da Shugaba Bola Tinubu, ya nada wato Jim Obazee, wanda zai gudanar da bincike kan zarge-zargen aikata almundahana a lokacin Emefiele a CBN.

Obazee, wanda Tinubu ya bai wa umarnin fara gudanar da bincike a kan Emefiele a ranar 28 ga watan Yulin 2023, ya gano yadda Emefiele ya bude asusun bankuna 593 a kasashen Amurka da  Birtaniya da kuma China, ba bisa ka’ida ba.

Ya kuma gano yadda aka saci dala miliyan shida kwatankwacin Naira biliyan 2.9.

Obazee bayar da shawarar hukunta Emefiele da wasu tsafffin jami’ansa 13, ciki har da maitaimakansa na shugaban babban bankin, saboda almundahanar da suka tafka.

Emefiele dai na ci gaba da fuskantar tuhuma a kotu, bayan laifukan da ake zarginsa da suka shafi mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da kuma karkatar da dukiyar kasa.