✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta tsare masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba 80 a Kwara

Gwamnatin Kwara za ta sa dokar ta-baci kan masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, a yayin da EFCC ta kama mutum 80 kan laifin…

Gwamnatin Kwara ta ce za ta kafa dokar ta-baci kan masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, a yayin da EFCC mai yaki da masu karya tattalin arziki ta cafke mutum 80 kan laifin a satar ma’adinai a jihar.

Kwamandan EFCC reshen jihar, Michael Nzekwe, ya ce hukumar ta kama masu hakar ma’adinan ba bisa ka’ida ba ne da moto makare da ma’adinan a sassan jihar a cikin watanni 10 da suka gabata.

Ya sanar da hakan ne a yayin karbar bakuncin Kwamishinan Ma’adinai na jihar, Abdulqawiy Olododo, wanda ya je ofishinsa da ke Ilorin, domin neman hadin kan hukumar.

Nzekwe, ya shaida wa kwamishinan cewa EFCC ta “gano wurare daban-daban a ssan jihar da ake hakar ma’adinai ta bayan fage, inda aka kama kalla mutum 80 da motoci makare da ma’adinan da suka diba a waatnni 10 da suka gabata.”

A cewarsa, “Allah Ya albarkaci kananan hukumomin jihar 16 da ma’adinai masu tarin yawa da sun wadatar su mayar da jihar mai dogaro da kanta, har su mayar da ita wata aljannar duniya”, idan aka sarrafa su yadda ya kamata.

Da yake mayar da jawabinsa, kwamishinan ya bayyana shirin gwamantin jihar na sanya dokar ta baci wajen yaki da barayin ma’adinai.

Don haka “take nmena hadin kan EFCC wajen tsara bangaren ma’adinan domin samun masu zuwa jari na cikin gida da na kasashen waje.