✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufai Ya Kai Ziyara Sakatariyar Jam’iyyar SDP

Ziyarar tasa ta soma yamutsa hazo, inda wasu ke alakanta ta da siyasar 2027.

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya kai wata ziyara  sakatariyar jam’iyyar SDP ta kasa da ke Abuja, a ranar Laraba.

Ziyarar dai kawo yanzu babu wanda ya san gaskiyar dalilin ta.

SDP na daga cikin jam’iyyun da suka shiga zaben 2023, wanda El-Rufai ya taka muhimmiyar rawa a cikin jami’yyar APC da ta yi nasara a jiharsa ta Kaduna da kuma matakin Shugaban Kasa. 

Sunan Malam Nasiru na daga cikin wadanda aka mika wa majalisa domin tantnacewa a matsayin minista, sai dai bai samu sahalewar majalisar ba, sakamakon wasu dalilai da har yanzu ba a bayyana ba. 

Bayan wannan tirka-tirkace El-Rufa’i ya yi batan dabo a siyasa, inda  ba a kara jin duriyarsa ba a siyasance sai wannan ziyara da ya kai ofishin jam’iyyar SDP.

Ziyarar tasa ta soma yamutsa hazo, inda wasu ke alakanta ta da siyasar 2027.