✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufai ya ki bude makarantu duk da umarnin Gwamnatin Tarayya

Makarantu biyu kacal za a bude a fadin jihar ranar Litinin

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce ba za a bude makarantu a jihar ba, duk kuwa da umarnin Gwamnatin Tarayya na bude su a ranar Litinin 18 a watan Janairu, 2021.

Babbar Sakaraten Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna, Phoebe Sukai Yayi, wadda ta ce jihar na nazarin yanayin yaduwar cutar COVID-19 a Jihar, ta ce wajibi ne duk makarantu da ke jihar, har da na Gwamantin Tarayya, su kasance a rufe har sai lokacin da Gwamnatin Jihar ta sanar.

“Muna fada da babbar murya cewa Jihar ba ta riga ta sanya ranar bude makarantu ba.

“Duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta sa ranar 18 ga Janairu, 2021 domin bude makarantu, Jihar ba da sa rananta ba tukuna.

“Muna lura da halin da ake ciki kuma za mu fitar da sanarwa game da hakan nan ga ba”, inji jawabin da ta yi ranar Lahadi.

Ta ce makarantun Gwamnatin Tarayya biyu kadai za a bari a bude a ranar Litininin 18 ga Janairu, 2021.

Makarantun su ne Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna (KADPLOY) da kuma National Open University (NOUN) da suka nemin izinin a bari dalibansu su rubuta jarabawa.

Game da Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) kuma, Ma’aikatar ta ce ba ta samu bukatar haka daga hukumar makarantar ba.

Ranar 18 ga watan Janairun ne dai Gwamantin Tarayya ta sanya domin bude makarantu don ci gaba da karatu bayan ta rufe su saboda sake bullar cotar COVID-19 a karo na biyu.