✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#EndSARS: An kona Babbar Kotu, an yi wa ma’aikatanta yankan rago

Daruruwan matasa da ake zargin bata-gari ne da sanyin safiyar Alhamis sun mamaye harabar Babbar Kotun birnin Asaba na Jihar Delta tare da banka mata…

Daruruwan matasa da ake zargin bata-gari ne da sanyin safiyar Alhamis sun mamaye harabar Babbar Kotun birnin Asaba na Jihar Delta tare da banka mata wuta.

Harabar kotun dai wacce take da gine-gine guda hudu da kuma dakin janareto da bangaren jami’an tsaro da kuma wasu sabbin motoci guda biyu duk sun kone kurmus.

Aminiya ta kuma gano cewa an yi wa wasu ma’aikatan kotun guda biyu yankan rago bayan da suka yi yunkurin hana bata-garin da suka tattaro takardun kotun da nufin cinna musu wuta.

A cewar wani ganau, ma’aikatan kotun dai sun kwace wasu daga cikin takardun kotun ne daga cikin tarin wadanda aka jibge kana aka banka musu wuta sannan suka yi kokarin guduwa domin mayar da su cikin kotun kafin bata-garin su kamo su tare da sassara su da adduna.

Wani da abin ya faru a kan idonsa ya ce matasan sun shafe kimanin sa’o’i biyu suna cin karensu ba babbaka a kotun.

Da Aminiya ta ziyarci wurin, ta iske jami’an sojoji sun kafa shinge a mashigar kotun, amma ba a hana mutane masu ababen hawa da masu tafiya a kafa su shiga.

Kazalika, jami’an Hukumar Kashe Gobara ta jihar sun hallara a harabar kotun ko da yake ba su tarar da ko da abu daya mai amfani da bai kone ba.

A daidai lokacin da wutar ke tsaka da ci kuma, gungun matasan sun wuce zuwa babban titin Nnebisi Road dake tsakiyar birnin suna rera wakokin zanga-zangar.

A ranar Larabar da ta gabata dai gwamnan jihar Ifeanyi Okowa ya sanya dokar ta-baci ta tsawon sa’o’i 48 bayan wasu bata-garin da suka fake da sunan zanga-zangar sun kona kayayyakin gwamnati da dama a jihar.

Gwamnan ya ce dokar za ta fara aiki ne tun da misalin karfe 6 na yammacin ranar Alhamis tare da sanar da rufe dukkan makarantun firamare da na sakandiren jihar har zuwa 2 ga watan Nuwamba mai zuwa.